Min menu

Pages

Ƙasa ɗaya tilo a Afrika da basu da ‘ATM’ na cirar kuɗi ko ɗaya a cikin ta.

 Ƙasa ɗaya tilo a Afrika da basu da ‘ATM’ na cirar kuɗi ko ɗaya a cikin ta.Akwai ƙasashe sama da 50 masu cin gashin kansu a nahiyar Afirka. Wannan shi ne daya daga cikin manyan dalilan da suka sa ake cewa Afirka na daya daga cikin nahiyoyin da suka fi yawan jama’a a duk fadin duniya.


Haka zalika, yana da mahimmanci a nuna cewa akwai wata ƙasa ta Afirka da babu Automated Teller Machines (ATM) ko ɗaya a cikin ta.


Ku biyo mu sannu a hankali domin gano wace kasa ce wannan kasa a Afirka da ba ta amfani da ATM domin cire daga banki kai tsaye.


Ƙasar Eritrea: Sunan hukuma na wannan ƙasa shine ‘State of Eritrea’. Tana yankin gabashin nahiyar Afirka.


Eritrea ta sami ‘yencin kai a ranar 27 ga Afrilu, 1993. Shugaban kasar Eritrea mai ci shine Isaias Afwerki. Ya kasance a ofis tun shekara ta 1993. Akwai ƙasashe da yawa a duniya waɗanda mutane za su iya yin amfani da na’ura ta atomatik domin cire a bankuna. Sai dai a cewar Hukumar Watsa Labarai ta Biritaniya, babu wata na’ura (ATM) mai ba da damar cire kuɗi a Eritrea.


Saboda haka, wannan ya nufin mutane dole za su iya cire kudi a cikin banki kawai.

Comments