Min menu

Pages

Shugabannin kasashen Afrika 18 da suka mutu kafin karewar wa'adinsu mulkinsu..

 Shugabannin kasashen Afrika 18 da suka mutu kafin karewar wa'adinsu mulkinsu. 



A Yayinda wasu kashe su akayi, wasu kuma sun mutu ne sakamakon cuta da suke fama da ita.


 Yar'adua, Gaddafi da sauran shugabannin kasashen Afrika 18 da suka mutu kan mulki gasu kamar haka;


 1. John Magufuli na kasar Tanzaniya: Ya mulki kasar na tsawon shekaru shida kuma ya mutu sakamakon ciwon zuciya a Maris 2021


 2. Pierre Nkurunziza na kasar Burundi: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 15, Ya mutu sanadiyar bugun zuciya a Yunin 2020



 3. Michael Sata na kasar Zambiya: Ya mutu a watan Oktoba 2014, ba'a bayyana abinda yayi sanadiyar mutuwarsa ba.


 4. Meles Zenawi na kasar Ethiopia: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 21 daga 1991 zuwa 2012. Ya mutu a Agustan 2012. ba'a bayyana abinda yayi sanadiyar mutuwarsa ba.



 5. John Atta Mills na kasar Ghana: Ya mulki Ghana daga shekarar 2009 zuwa lokacin da ya mutu sanadiyar bugun jini da cutar daji a 2012.


 6. Bingu wa Mutharika na kasar Malawi: Ya mulki kasar ne shekaru takwas kuma ya mutu a sanadiyar bugun zuciya a shekarar 2012.


 7. Malam Bacai Sanha na Guinea-Bissau: Ya mulki kasar na tsawon shekaru hudu kacal kuma ya mutu sanadiyar cututtuka da dama a 2012



 8. Moammar Gadhafi na kasar Libya: Yan tawaye sun kashe shi bayan mulki tsawon shekaru 42 a Libya a shekarar 2011.


 9. Umaru Musa Yar’Adua na Najeriya: Ya mulki Najeriya na tsawon shekaru uku kacal kuma ya mutu a sanadiyar cutar pericarditis a shekarar 2010



 10. Joao Bernardo Vieira na Guinea-Bissau: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 31 kuma an kashe shi a watan Maris na 2009.



 11. Omar Bongo na kasar Gabon: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 42 kuma ya mutu a Yunin 2009 sanadiyar cutar dajin hanji.


 12. Lansana Conte na kasar Guinea: Ya yi fama da cutar Siga kuma ya mulki kasar na tsawon shekaru 24. Ya mutu a 2008.


 13. Levy Mwanawas na kasar Zambiya: Ya mutu yayin wa'adinsa na biyu a Agustan 2008


 14. Gnassingbe Eyadema na kasar Togo: Ya mulki kasar na tsawon shekaru 38 kuma ya mutu a 2005 sanadiyar bugun zuciya.


 15. Muhammad Egal na kasar Somaliya: Ya mutu a 2002 ana yi masa aikin Tiyata a kasar Afrika ta kudu.



 16. Laurent Kabila na kasar Congo: Ya mutu a shekarar 2001 lokacin wani dogari ya bindigeshi a fadar shugaban kasa


 17. Ibrahim Mainassara na kasar Nijar: Wasu da ake zargin dogarawanshi ne suka bude masa wuta har lahira a shekarar 1999



 18. Sarkin Maroko, Hassan II: Ya mulki Kasar ta Maroko tsawon shekaru 38 kuma jinin Manzon Allah (S.A.W) ne. Ya mutu a 1999.

Comments