Min menu

Pages

Yara 5 Mafi Arziki A Duniya A Shekarar 2022

 Yara 5 Mafi Arziki A Duniya A Shekarar 2022


1. Gimbiya Charlotte - Tana da darajar dala biliyan 5 Gimbiya Charlotte ta Cambridge ta doke dan uwanta inda ta zama yarinya wanda tafi kowa arziki a duniya da kimanin dalar Amurka biliyan 5.

  An haife ta a ranar 2 ga Mayu, 2015, duk da cewa su biyu ne iyayensu suka haifa, sai dai iyayen nasu sun yanke shawarar su baiwa Gimbiya Charlotte dukiyar fiye da dan uwanta.

  Mahaifinta Yarima Charlotte shi ne na hudu a jerin masu jiran gadon sarautar Burtaniya.


2. Yarima George Alexander Louis - Yana da darajar dala biliyan 3  Yarima George Alexander Louis yana da kimanin dala biliyan 3 kamar masu ƙididdiga suka bayyana a shekarar 2021 kenan idan aka yi duba yar uwarsa ta fi arziki da dala biliyan 2 kenan.

  An haife shi a ranar 22 ga Yuli, 2013, Yarima George kuma ana kiransa da Yarima George na Cambridge.

 Yarima George shine ɗan fari a wajen Yarima William Duke na Cambridge da mahaifiyarsa Catherine Douches. Kanwarsa Gimbiya Charlotte ita ma tana cikin manyan attajirai a duniya a yau.


3. Blue Ivy Carter – Yana da darajar dala biliyan 1  Blue Ivy ce ta 3 a jerin yara mafiya arziki a Amurka. Babu shakka, babu wata hanya mafi kyau da sauƙi don zama mai arziki fiye da a haihi mutum cikin iyali mai arziki.

  Blue Ivy ta kasance daya ce daga cikin irin wadannan yara inda ta kasance yarinya mai sa'a a rayuwarsa. Inda ta fito daga dangin waƙan hip hop mafiya wadata, wato Beyoncé da Jay-Z.

 An yi imanin cewa dukiyarta ta haura darajar dala biliyan 1 kuma tana ci gaba da haɓaka, kuma ana sa ran za ta iya rike yarinya mafi arziki a Amurka har na dogon lokaci.

  Sai dai wannan hasashen zai iya cika ne kawai bayan iyayenta sun mutu, saboda za ta gaji biliyoyin kadarori da kayan jin daɗi.


4. Suri Cruise - Yana da darajar dala miliyan 800  Suri tana cikin rukunin yara mafiya arziki a duniya, iyayenta Tom Cruise da kuma mahaifiyarta Katie Holmes attajirai ne.  Kamar sauran yaran da suka fi kowa wadata, yawancin dukiyar da aka lissafa zata gajesu ne da zarar iyaye sun mutu.

  Ita dai Suri tana da shekaru 15 da haihuwa, sannan tana kan gaba a jerin yara masu arziki a duniya.


5. Stormi Webster – Tana da darajar dala miliyan 726  Stormi Webster 'yar Amurka ce, kuma ƴa ce ga ɗan wasan kwaikwayon nan ne, kuma ɗan kasuwa wato Kylie Jenner da Travis Scott.  

   Stormi ta samu farin jini a wajen iyayenta tun kafin a haife ta. Daga baya, ta ƙara samun farin jini, mai yiwuwa ta zarce mahaifiyarta da mahaifinta. Tana da darajar dala miliyan 726 kamar yadda aka bayyana a cikin shekarar  2021.

Comments