Min menu

Pages

Wasu Tsofaffin Shugabanni Kasashe Da Aka Dauresu A Gidajen Yari Saboda Aikata Laifin Cin Hanci Da Rashawa

 Wasu Tsofaffin Shugabanni Kasashe Da Aka Dauresu A Gidajen Yari Saboda Aikata Laifin Cin Hanci Da Rashawa


 Daya daga cikin manyan kalubalen da duk wani shugaba ke fuskanta shi ne nisantar cin hanci da rashawa.  Sai dai yana da matukar wahala a samu shugaban da yake tsallake wannan siraɗi na cin hanci da rashawa.


 Abin baƙin cikin ma shine, akwai wasu shugabannin duniya waɗanda ba za su iya hanku cin hanci amman kuma suyi ƙoƙarin hana al'ummar da suke mulka..


 Wasu daga cikin wadannan shugabannin ba su yi nasarar tserewa Shari'a ba, domin kuwa an yanke masu hukunci daidai da abinda suka aikata.  A yau za mu yi duba ne ga wasu daga tsaffin shugabannin Duniya guda 3 da ake tsare da su a gidan yari bayan an same su da laifin cin hanci da rashawa.


 1. Amado Boudou. Amado ya kasance ya riƙe mataimakin shugaban kasar Argentina daga shekara ta 2011 zuwa 2015. Bayan ya bar mulki ne, sojoji suka taso masa cewa gwamnatinsa na cike da almundahana kuma aka kai shi kotu.  Tabbas Amado yayi kokarin musanta zargin cin hanci da rashawa.

 Wani abin sha’awa, shekaru 3 kacal bayan ya bar mulki, aka yi bincike aka kuma same shi da laifin cin hanci da rashawa a shekarar 2018. An yanke masa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari tare da tarar dala miliyan 10.  Hukumomin Argentina sun kuma haramta wa Amado sake rike wani mukami na gwamnati. 


 2. Antonio Saca. Antonio shi ne shugaban kasar El Salvador daga shekara ta 2004 zuwa 2009. An samu Antonio da laifin cin hanci da rashawa a shekarar 2018 kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.


 3. Almazbek Atambayev. Almazbek ya riƙe muƙamin shugaban kasar Krygyzstan daga shekara ta 2011 zuwa 2017. An yanke masa hukunci a shekarar 2020 bayan samunsa da laifin cin hanci da rashawa.  An yanke masa hukuncin daurin shekaru 11 a gidan yari saboda samunsa da laifin cin hanci da rashawa.  Bayan ɓoye-ɓoyen da ya dinga yi saboda yunƙurun da sojoji suka so yi, an rasa jami'an soji da dama a wannan farmaki, a ƙarshe dai an tura shi kurkuku a ranar 10 ga Oktoba, 2020.

Comments