Min menu

Pages

Kasashe 5 A Duniya Da 'Yan Sanda Basa Rike Bindiga

 Kasashe 5 A Duniya Da 'Yan Sanda Basa Rike Bindiga
 1- Ingila Mutane da yawa sun yi mamakin jin cewa rundunar 'yan sandan Burtaniya ba sa riƙe bindiga duk da matsayinta, da kuma ƙarfin siyasa, zamantakewa da tattalin arziki.


 A gaskiya Birtaniyya suna yin aiki ne a ƙarƙashin ƙa'idar cewa ya kamata 'yan sanda su kasance masu kusanci da jama'a a matsayinsu na masu kare ƴan ƙasa maimakon farautar masu laifi wannan doka an jaddadata tun a karni na 19.


 Lokacin da aka tambayi wani jami'i game da ɗaukar bindigogi yayin da suke bakin aiki, 82% na jami'an 'yan sanda sun ce basu iyawa domin basu saba ba.


 Sai dai duk da haka adadin mu'amalar da ke tsakanin 'yan sanda da masu aikata laifuka a Burtaniya ya yi ƙasa sosai fiye da kowace katsa ta G7.


 2- Norway


 

 Norway na ɗaya daga cikin ƙasashe 19 da jami'an tilasta bin doka (Yan sanda) ba su riƙe bindiga.


 Jami’an ‘yan sanda ba sa riƙe bindugu a lokacin da suke sintiri, amma suna yawo da su sai dai suna kulle bindugun nasu ne a cikin motocin sintiri.


 Kafin su fiddo da bindigun nasu daga cikin motocin sintirin dole ne sai sun jira izini daga shugaban ‘yan sanda ko kuma wani mai ikon faɗa aji a cikin ƙasar.


 3- Iceland A Iceland, jami'an sintiri ba sa ɗaukar bindiga a cikin wannan ƙasar, maimakon haka jami'an suna dauke da barkonon tsohuwa da sanduna masu tsayi.


 Kusan kashi ɗaya bisa uku na ƴan ƙasar a Iceland suna da  makamai.  Sai dai duk da irin wannan jama'a masu tarin makamai, ba kasafai ake aikata laifuka ba, kawai suna amfani da bindigogin sune domin farauta.


 4- New Zealand


 

 Jami'an 'yan sandan ƙasar New Zealand suma suna amfani da barkono mai sanya hawaye da kuma sanduna, duk da cewar suna da bindigogi  ajiye a cikin motar su wanda za a iya amfani da su idan uzirin haka ta kama.


 5- Ireland Tun lokacin da aka kafa rundunar 'yan sanda a Jamhuriyar Ireland a shekarar 1923, ta kasance rundunar da basa riƙe bindigu, kuma fiye da kashi uku cikin hudu na rundunar ba sa daukar bindigogi akai-akai.


 Akafi cikin ‘yan sanda mai muƙamin ASP ne kaɗai yake da ikon riƙe bindiga, amman sauran sai dai su riƙe   barkonon tsohuwa a matsayin makamansu na yau da kullun.

Comments