Min menu

Pages

Ƙasashe 3 da suke kan gaba wajen kera jiragen sama

 Ƙasashe 3 da suke kan gaba wajen kera jiragen sama



Jirgin sama har yanzu yana daya daga cikin abubuwa masu kyau kuma wanda mutum bil'adama yayi amfani da basira wajen kerawa, domin anyi amfani sosai da kimiyya da fasaha wajen kera jirgin sama.


Duk mutumin da ya kalli yadda jirgin sama yake da kuma yadda aka kerashi har yake iya tashi sama duk da tsananin girmansa yasan anyi basira sosai a gurin.

Jirgin sama wani abu ne da ake tafiye tafiye dashi tsakanin kasa zuwa kasa, ko kuma gari da gari, sannan kuma kala kala ne akwai manya masu daukar taron mutane akwai kuma kanana sannan akwai wanda ake yi domin yaki da dai sauransu.


To yau dai cikin shirin namu zamu kawo muku jerin wasu ƙasashe guda uku wanda suka fi ko wacce kasa masana'antar kera jirgin sama kuma sune kan gaba wajen kerawa.


1 America :- Kasar America wacce ake ce mata united State of America ita ce ta farko kuma babba a jerin kasashen da suke kera jirgin sama na tafiye tafiye da kuma na yaki.


Kasar ta kware matuka wajen kera duk wasu nau'ikan jirage da suke tashi sararin samaniya.


2 France Kasar France ita ce ta biyu a jerin kasashen da suke kera jirgin sama sannan kuma wanda suke da masana'antun da ake kerawa masu tarin yawa.


3 Germany kasar Germany ita ce ta uku a jerin kasashen da suke da manyan masana'antun kera jirgin sama, kuma tana sahun farko na kasashen da suke kerawa.


Comments