Min menu

Pages

Ƙasa ɗaya tilo a duniya da basu da fursunoni a gidajen yarinsu.

 Ƙasa ɗaya tilo a duniya da basu da fursunoni a gidajen yarinsu. Haƙiƙa zai yi wahala wasu mutanen su yarda da ni, amman ga masu bincike irina ba wani abin mamaki bane, na cewar akwai ƙasa ɗaya tilo wadda basu da fursuna ko ɗaya a gidajen yarinsu. Kasancewar bama a iya ƙasar mu ta Afrika ba, a duniya yawaitar aikata laifuka yana ƙara yawaita.


 Sai dai wani abin mamaki shine, duk da yawaitar aikata laifuka da ake yi a duniya ƙasar Netherlands tana da ƙarancin masu aikata laifuka a cikin ƙasar.


 Wani bincike da muka yi shine, a cikin Ƙasar Netherlands, mutane 19 ne kawai aka daure shekaru takwas da suka gabata, kuma babu masu laifi da yawa a cikin ƙasar yanzu, a wannan shekara da muke ciki ta 2022.

  A cewar rahoton na Telegraph UK da aka buga a cikin shekarar 2016, Ma'aikatar Shari'a ta Holland ta ba da sanarwar cewa yawan aikata laifuka zai ragu da kashi 0.9 cikin ɗari a shekaru biyar masu zuwa.


 Rahotannin da ke fitowa daga kasar na nuni da cewa, kasar Netherlands ta rufe gidajen yarin ta da dama tare da cike sauran 'yan tsiraru da wasu fursunoni na kasashen waje.  Abin da ya sa ake yin irin wannan abin ban mamaki shi ne saboda ƙarancin ɗaurarru a gidan kurkuku, ko kuma adadin da ƙasa ke ɗaure masu laifinta.


 Ƙasar dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka yi imanin cewa, maimakon a hukunta masu aikata laifuka, kamata ya yi a gyara su domin a taimaka musu, su yi rayuwa mai inganci.  A cewar wani bincike, kusan rabin dukkan masu aikata laifuka sun daina aikata sabbin laifuka sakamakon hakan.


 Kasar Netherland ta rage yawan gidajen yari har zuwa inda ake mayar da gidajen yarin da ba su da kyau su zama cibiyoyi masu amfani da zamantakewa kamar makarantu da matsugunan ‘yan gudun hijira. Duk da yake akwai matsaloli da yawa a cikin ƙasar ta Netherlands tare da muggan kwayoyi kamar tabar wiwi da hodar Iblis, hukumomi sukan mayar da hankali kan masu shigo da kayayyakin maimakon masu amfani da su, wanda ke haifar da raguwar masu aikata laifukan.


 Duk da kasancewar rufe gidajen yari na iya janyo asarar ma’aikata 2,000, inda 700 daga cikinsu ne kacal ake mayar da su wasu mukaman gwamnati.  A daya hannun kuma, ana ganin cewa kasar ta samu nasara a matsayin tsari gwamnati, da kuma ‘yan kasa.

Comments