Min menu

Pages

Zamu nemawa duk wacce akai lalata da ita kafin a sata a film hakkinta inji Nafisa Abdullahi

 Zamu nemawa duk wacce akai lalata da ita kafin a sata a film hakkinta inji Nafisa Abdullahi



Duk Wacce Aka Yi Lalata Da Ita Kafin A Sa Ta A Fim Ta Fito Ta Fada Zamu Nema Mata Hakkin Ta 


A ko wane profession akwai matsaloli daban daban da mutane ke fuskanta, akwai Masu cuta, akwai Kuma Wanda ake cutarwa.


Zantuttukan da Naziru Ahmad yayi, Serious allegations ne da ba’a daukan su da sanyi ko ah ina ne, ah ciki har da ‘Sexual Assault’ Wanda shine dalilin da ya sa na saka Kaina ah cikin abinda bai shafe ni ba….. Amma Kuma idan akayi la’akari da abinda ya fada, ya shafe ni tunda mace ce ni.


Idan abinda yake fada Gaskiya ne Kuma yana da hujjoji da Kuma shaidu, ina cikin mutanen da suke so su san su waye Masu yin hakan! Tunda ya fadawa duniya cewa ga abinda ake yi, toh karshen adalci wa Wanda aka zalunta shine mu san su waye Kuma mu dauki Mataki akan su, Dan a cikin Laws din mu na kasar nan da Kuma film industry din, babu inda it’s acceptable to say a lady should sleep with you for films. There are consequences and the people who’re guilty should be seriously punished.


Daga Karshe Kuma, duk macen da ta san an taba ce Mata to give herself for films, fight for your rights and tell us su waye, because if you don’t speak up, baza ah taba samun gyara ba.



Comments