Min menu

Pages

Wasu daga cikin sabin dokikin zabe da shugaba Buhari ya sanyawa hannu a jiya..

Wasu daga cikin sabin dokikin zabe da shugaba Buhari ya sanyawa hannu a jiya..1- Dole jam'iyun siyasa su kammala zaben cikin gida wato primary election wata shida kafin zabe. Kenan ba za'a wuce watan August ba na wannan shekarar za'a san yan takara tun daga matakin shugaban kasa har kasa a duk jam'iyun. Wannan zai bada damar a kammala duk wata shari'ar rikicin zaben fidda gwani kafin zabe, ba kamar yadda aka saba ba a baya a shiga zabe ba'a ma san waye dan takara ba saboda ana kotu....


2- Sabuwar doka ta bawa yan takara isheshen lokaci domin yin yakin neman zabe, daga sanda aka gama zaben cikin gida zuwa sanda za'ai zaben duk gari akwai wata 'dai-'dai-'dai har wata biyar! Daya daga cikin takaicin da nake a baya shine yadda yan takara suke wa yan dangwale shan ruwan tsuntsaye lokacin yakin neman zabe, misali sai kaga dan takarar shugaban kasa idan yaje wata jihar, daga fadar Sarki sai gurin gangami daya kawai zai je, wani ma bai fi yayi magana ta minti biyar ba a watse, yan dangwale da sauran masu ruwa da tsaki basu samu damar jin manufofi da kudurin dan takara ba. Wannan shi yasa muke yin zaben tumin dare....


3- Sannan wani muhimmin abu da dokar ta kunsa shine a yanzu ya zama wajibi a bawa hukumar zabe kudaden gudanar da zabe shekara daya kafin zabe domin su yi shiri da wuri na zaben, ba sai lokaci ya kure ba a zo ana ta tsilla tsilla....


4- Akwai kuma maganar aringizon kuri'u, wanda dokar ta ce duk inda aka zuba kuri'u suka fi yawan wadanda aka tantance a ranar zabe, toh wannan zai zamo abin dubawa wajen yanke hukuncin wanda ya ci zabe...


5- Wani muhimmin abu shine maganar aika sakamakon zabe ta yin amfani da na'urar zamani. A da idan aka kammala zabe a mazaba aka sanar da shi, wajen daukar sakamakon akai wajen tattara sakamakon ko na karamar hukuma ko na jiha, ana samun wasu suna canza wannan sakamakon, dan haka a yanzu nan take za'a aika shi kai tsaye tun daga mazaba ta hanyar amfani da na'urar zamani....


6- Hakazalika dokar ta ce duk wani mai rike da mukamin gwamnati nadadde dole ne ya ajiye kujerar sa kafin ya zama dan takara ko kuma delegate din da zai yi zabe. Wannan na daya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen dakile yan takarar da basa tare da jam'iya mai mulki ko kuma jam'iyar adawa. Duk da kamar wannan shugaba Buhari yayi kira ga majalisa akan a gyara shi kamar ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar....


7- Sannan akwai maganar bada kulawa ga masu bukata ta musamman a ranar zabe, kamar makafi domin ganin an basu dama suma an dama da su a harkar zabe musamman wajen zaben raayin su....

Comments