Min menu

Pages

Wasu abubuwa guda uku da suke ciwa yan Nigeria tuwo a kwarya wanda shugabanni suka kasa magancewa

 Wasu abubuwa guda uku da suke ciwa yan Nigeria tuwo a kwarya wanda shugabanni suka kasa magancewa



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu koda yaushe muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da jerin wasu abubuwa guda uku da suke ciwa yan Nigeria tuwo a kwarya wanda har yanzu shugabanni suka kasa magancewa.


Nigeria kasa ce guda daya data kasance babba a nahiyar Africa kuma wacce tai suna sosai a duniya baki daya, wacce ta tara abubuwa masu yawa wanda ba duka kowacce kasa bace keda irin wadannan abubuwan.

Kamar kasar noma, dukiyar karkashin kasa irin su man fetir da sauran albarkatun kasa, haka Nigeria ta tara shugabanni wanda suke iya fada aji ko ayi amfani da maganarsu a fadin Africa baki daya.

To amma akwai wasu abubuwa da suke ciwa yan kasar tuwo a kwarya wanda kuma har yanzu an gagara magance musu tsawon lokaci.


Tsaro:- Duk da kasancewar Nigeria tanada karfi wajen jami'an tsaro tun daga na sama dana kasa da kuma na ruwa amma yan kasar kullum kuka suke saboda yadda matsalar rashin tsaron tai musu katutu koda yaushe suna cikin jimami na rashin tsaro da kuma tashe tashen hankula a yankuna da dama na cikin kasar.

Mutanen dake cikin kasar har yanzu suna mamaki na yadda akai hakan yake faruwa na karancin tsaron da kasar ke fama dashi duk da kasancewar akwai bila'adadin na jami'an tsaro wanda suke a kasar.


Talauci da tsadar rayuwa:- Yan kasar sun kasa gane laifin waye a tsakaninsu da gwamnati domin wani lokacin gwamnati na ganin laifin yan kasar ne da basa iya tashi su nema suma kuma yan kasar na ganin akwai laifin gwamnati da bata tallafa musu duk kuwa da cewar yanzu akwai hanyoyi da dama da aka fitar na taffawa yan kasar da yawa domin su dogara da kansu.


Kayan lefe da kuma kuma kayan dakin amarya:- Wannan wata babbar matsala ce da take ciwa yan kasar tuwo a kwarya musamman yan arewacin kasar, mutane suna ta cewar a soke yin lefe musamman samari masu son yin aure amma basu da halin yi idan har sai sunyi lefe, haka zalika wasu daga cikin yan matan ma suna son yin aure amma gidansu basu da damar yin kayan daki wannan yasa suke zaune a gida ba tare da sunyi aure ba wanda wannan ba karamar matsala bace da take damun mutane.

Ya kamata a sanya dokar da zata soke duka wadannan abubuwan guda biyu kayan daki da kuma lefe domin mutane su samu damar aure, ya kasance miji za'a kai masa mata gida da katifa kawai da kwanukan dafa abinci shi kuma idan yanada hali ya sayi gadon da za'a dora katifar akai shikenan.

Idan akai haka komai zai tafi daidai.

Bayan haka akwai wasu matsalolin wanda su kuma masu sauraro muke so suyi mana bayaninsu.

Mun gode.

Comments