Min menu

Pages

Wani gari wanda basa amfani da kudi wajen yin kasuwanci a Nigeria

 Wani gari wanda basa amfani da kudi wajen yin kasuwanci a NigeriaKo kunsan akwai wani garin a dake cikin Nigeria wanda su har yanzu basa amfani da kudi wajen gabatar da harkokin kasuwancinsu saidai suna bada wani kayan sannan su karbi wani kayan, ina nufin idan kaje kasuwar da kayanka saidai ka samu wani da yake bukatar irin kayan naka ka bashi sai ya baka nasa wato kasuwancin da ake cewa bani gishiri in baka manda kenan?

Idan baku sani ba cikin wannan bidiyon zamu sanar daku sunan garin da kuma jihar da yake a Nigeria, amma kafin nan idan wannan shine farkon shigowarku wannan gidan ku duba sama za kuga an rubuta follow saiku danna domin kuyi following din wannan Page din namu.


Kauyen Esuk MBA wani dan karamin guri ne da wasu mutane ke zama sannan kuma da  kasuwa a gurin wacce take ci sau daya a sati, kauyen yana karkashin karamar hukumar akpabuyo ne dake jihar Cross rivers, wanda su har yanzu suna gabatar da kasuwancinsu ne kamar na zamanin baya wato wanda ba'a amfani da kudi.


Inda suke daukar kayansu sukai kasuwa sai kuma su samu wanda yake son kayan ka bashi idan kayan da yake gurinsa irin wanda kake so ne saika karbi nasa.


Mutanen dake zaune a wannan gurin sunce suna matukar jin dadin wannan kasuwancin da suke.


To jama'a anan zamu dakata mu hadu daku a wani sabon shirin.


Comments