Min menu

Pages

Wani gari da ba'a amince mata su haihu ba

 Wani gari wanda ba'a yadda mace ta haihu a cikinsa ba, kuma ba'a binne mutum a cikin garin idan anyi mutuwa.Kusan kowacce kabila sunada nasu abubuwan da suke gabatarwa a matsayin al'ada wanda suka gada tun iyaye da kakanni.


Wasu abinda suke gabatarwar bashi da laifi, yayinda abubuwan da wasu kuma ke gabatarwa ko kadan bayyi tsari ba.


A yau muna tafe da labarin wani gari a kasar Ghana mai suna MAFI DOVE inda ba'a amince mace ta haihu a cikin garin ba.


Garin bashi da girma sosai sannan bashi da yawan mutane saidai dabi'ar da suke da ita ne yasa ake bada labarinsu domin sun canfa cewar barin haihuwa a garin ka iya kawowa faruwar wasu abubuwa na yawaitar zunubai.


Sannan idan mutum ya ziyarci wannan ƙauyen akwai wasu abubuwa da zai rika cin karo dasu masu ban mamaki wanda garin suka hana aikatawa kamar kiwon dabbobi da kuma ficewar tsuntsaye ta saman garuruwan.


Ko kadan ba'a kiyon dabbobi a garin kuma ba'a amince a kawo dabba ta kwana ba amma an yadda ana kawota a yanka ta.


Sannan koda mutum ya mutu a garin basa binne shi saidai su dauki gawar suyi tafiya mai nisa zuwa wani garin sannan su binne domin sun canfa duk ranar da suka binne mutum a garinsu ko suka bari wata mace ta haihu a cikin garin shikenan masifu sun dinga faruwa dasu.


Dan haka daga zarar mace cikinta ya girma to zata tafi can wani garin harta haihu, bayan ta haihu saita samu wasu kwanakin acan saita dawo.


Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.

Comments