Min menu

Pages

Russia ta tura wani babban sako zuwa ga Nigeria

 Russia ta tura wani babban sako zuwa ga NigeriaKamar yadda bayanai suka rawaito cewar anyi zama da ambassador na Russia ranar litinin a Abuja wanda aka Tattauna akan rikicin kasar da suke da Ukraine, harma ake tunanin Anji ana cewa ana rokon kasar ta Russia cewar ta fitar da sojijinta daga kasar ta Ukraine.

Mutane daga cikin kasar Nijeriya suna ta tattaunawa kan cewa me yasa kasar Nigeria zata sanya baki ga Russia bayan shugaban kasar ya nuna baya son kowacce kasar tayi azarbabin sanya baki idan har ba so suke azo ta kansu ba.

To saidai ambassador din kasar ta Russia ya fito yayi karin bayani cewar Nigeria bata daga cikin sahun kasar da za suyi yaki da ita, domin ko babu komai danganta mai karfi a tsakani wanda suke ganin kasar a matsayin abokiyar kasar su kamar yadda Alexei Shebarshin din yace.

Comments