Min menu

Pages

Mata sun tsani duk wani Na miji mai wadannan halaye 8 din

Mata sun tsani duk wani Na miji mai wadannan halaye 8 dinAkwai nau'ikan halaye  guda takwas da duk wata mace ta tsani na miji mai aikata su, domin daya daga cikin halayen kan iya sanyawa mace taji bata son mutum koda suna soyayya kuma a koda yaushe zata iya barinsa.

Dan haka zamu zayyano muku halayen guda takwas wacce duk wata mace ta tsani masu aikatasu


1.  Yes Man : Ba zaka  taba farantawa mata ba idan ka kasance 'yes man ne Kai, wato wanda baya jayayya dasu ba, saidai ka kasance duk abinda mace tace dakai ka amince mata'. Sai dai idan tana ƙoƙarin yin amfani da kai don cimma wata manufa ta son zuciya, ba za ka taɓa burge ta da halin ka na eh angama ba.


Mutum mai jayayya baya saki. (Rashin yarda): Wasu mazan kawai suna son yin jayayya ba tare da ƙarewa ba kuma suna jin daɗin cin nasara kowace jayayya amma mai wuyar gaskiyar ita ce, ba za ka taɓa faranta mata da wannan hali ba. Mata suna ƙin maza masu jayayya mara iyaka da kuma maza waɗanda kuma suke ƙoƙarin gyara su koyaushe da cikakkun bayanai marasa mahimmanci.Na miji mai girman Kai : Babu macen da ke son namijin da a kullum yake neman wata dama ta rage mata daraja. Idan kana da wannan hali, to ba za ka taɓa burge ta ba. Mata suna ƙin maza waɗanda ke sa su ji cewa suna cikin ƙananan jinsi. Daraja kenan
Na miji mai shaci fadi: yana da sauƙi ga mace ta ta dage Kai ga maza masu shaci fadi ko yawan sanin abinda mace take yi a koda wanne lokaci, misali Mai son dole sai yasan abinda mace take ci kowace safiya, ko kuma yana yawan ce mata tayi abu kaza alhalin kuma kuma batai ba.


Mutum ya dinga abu kamar jariri (kuruciyar karfi da yaji): Wasu mazan har yanzu suna zama kamar jarirai kuma hakan yana gajiya tare da batawa mata rai. Mata ba sa son maza masu aikata butulci da dabi'ar yarinta. Don haka in kana son ka burgeta, to akwai bukatar ka girmama kanka sannan ka zama cikakken namiji.
Mai neman mace ta tausaya masa: wasu mazan kawai suna son neman a tausaya musu kuma wannan dabi'a ce da mata suka ƙi. Amincewa da iko a cikin namiji shine abin burgewa kuma da gaske wanda kana buƙatar sanin wannan idan kana son ka burge mata.


Na miji marar cika magana : Wasu mazan sun fi iya ƙwarewa a kalamai ta yadda kullum suke jawo mata zuwa garesu, amma matsalar ita ce, matan ba su daɗe tare da su ba. Daga lokacin da su ka gane mutum ne wanda baya cika maganarsa, za su rabu da kai. Mata ba su son wanda baya cika maganarsa


Na miji mai muguwar halayya: Wasu mazan su na da muguwar halayya kuma mata sun fi tsanar irin wadannan mazan. Yana da kyau ka koyi kyakkyawar halayya in kana so ka burge mace. Yawan sosa gabanka yayin magana da mace kuskure ne babba. Ka koyi dabi'a mai kyau tabbas za ka burgetaKarshe.

Comments