Min menu

Pages

HIRA TA MUSAMMAN DA MARUBUCIYA HAJARA AHMAD MAIDOYA _(OUM NAS)

HIRA TA MUSAMMAN DA MARUBUCIYA HAJARA AHMAD MAIDOYA _(OUM NAS)



Jigawa state writers association




Wasu daga cikin tambayoyin da akai mata da kuma amsar data bayar

1. Za mu son jin takaitaccen tarihin baƙuwarmu?


Assalama alaikum wa rahmatullah.

  Barkanmu da war haka, barkanmu da kasancewa da ku 'yan uwa.

1- To da farko dai sunana Hajara Ahmad Maidoya, An haife ni a garin Haɗejia, na yi karatu primary a Usman bn Affan daga nan na tafi sikandire a kwalejin 'yan mata dake ƙaramara hukumar Kaugama._  

   Na gama a shekarar 2009.

  Na yi aure a 2010 yanzu ina da yara huɗu. Na kuma kammala karatuna na Diploma a Binyaminu Usman polytechnic.

2. Me ya ja hankalinta ta fara rubutu?*


2- Na kasance ma'abociyar karance-karance a lokacin da ina sikandire, haka kuma ina mutuƙar son darasin Hausa.

   Wasu lokutan na kan zauna na yi rubutu, wadda a kan hakan yayata ta sha kai ƙarana gida.

 Daga ƙarshe saboda matsaloli daga gida, na haƙura da rubutun.  

  Kwatsam sai a ka samu ci gaba a media, na buɗe wani grp na Islamiyya muna ɗan tunatarwa daidai gwargwado, to sai na kula hankulan mutane ya rinjaya a kan karance-karance littafin Hausa. Daga nan kawai sai na yanke tunanin idan ina son isar da saƙo ga Al'umma to dole sai na yi tafiyar zamani nima, mussaman a yanzu da basa buƙatar wa'azi na kai tsaye, sun fi gane a haska musu madubin rayuwar da ke tafiya a cikin Adabi._

  Daga nan na faɗa rubutu a Media.


3. Shin ko ta fuskanci ƙalubale a harkar rubutu?


3-  Tabbas na fuskanci ƙalubale mai yawa. Musamman daga 'yan gidanmu, 'yan uwana da suke min kallon marar aikin yi. 

  Wasu lokutan har tambayata suke 'Anya ina aiki a gidana?' Wasu lokutan a kirani da kalmar 'Wahalalliya' 😃

  Lokacin har na fara tunanin lallai ni wahalalliya ce fa da gaske.😂  

  But Alhamdulillah dai a yanzu, komai ya wuce, suna ta ganin ba wahala ba ce, Fasaha ce, kamar dai yadda HIKIMA ZINARIYA ce ba'a samunta a sauƙi._


4. Ta taba fitar da littafi in eh ya sunansa in a'a me yasa?


4- Gaskiyan ban taɓa fitar da littafi ba. Saboda ni, tunanina ma bai taɓa bani zan fitar da shi ɗin ba.

  Amma a yanzu ina niya, yana tafe da yardar Allah.



5. A littafan da ta rubuta wanne bakandamiyarta?


_


6. Me za ka iya cewa game da rubutu a online cigaba da koma baya?

6- Eh to a yanzu zan iya cewa an samu ci gaba a rubutun online, idan na yi la'akari da a baya muna yinsa ne a kyauta. Saɓanin a yanzu da marubutan suke yin na kuɗi, kuma ana siya.

   Ƙarin daɗawa da yawa a cikin marubutan Publisher yanzu sun dawo suna yin na online, sai kuma yawaitar marubutan da aka samu. Wannan babban nasara ce sosai.

  Koma bayan kuma da aka samu, bai wuce yadda wasu basa inganta rubutunsu ba, wasu kawai suna rubutun ne dan su yi suna, amma ba dan sun san abin da suke rubutawar ba.  

  Misalin marubutan da suke rubutun batsa._


 7. Shin ko kin taba nasara a harkar rubutu da ba za ki taba mantawa da ita ba?


7- Gaskiya dai, Nasarata ta farko lokacin da na ci Gasar da ƙungiyata ta Nagarta ta sa mana na iya 'ya'yan ƙungiyar.

  Ban taɓa tunanin yin nasara a gasar ba, amma abin mamaki aka kirani ana sanar min ni na ci.  Abin ya ban mamaki na yi ƙaramin hauka da ihu.

  Musamman idan na tuna akwai waɗanda suka fini jimawa da gogewa a rubutu a cikin ƙungiyar.


8. Me za ki iya cewa game da yawaitar samun rubutun batsa a rubutu? Wanne hanyoyi za ki bayar na daƙile hakan?



8- Na kan rasa tunanin da ya shiga hankalin mutane a kan rubutun batsa. Amma kuma idan na nisa sai na tsinkayi suna yin hakan ne dan samun ɗaukaka da kuma mabiya a rubutun, waɗanda wannan zugar da suke musu kamar suna rura musu wata ƙofa ce da zata shigar da su wuta.  

  Akwai abin mamaki idan aka duba yawanci masu rubutun batsan sai ka gansu yara ne, wasu ma abin haushi ko aure ba su yi ba, 'Yan mata ne.  Kaɗan ne ake samu a cikin matan auren na yin irin waɗan nan rubutun.

  Gaskiya a ganina duk wani mutum mai hankali, wadda yasa mai yake yi, to yana da kyau ya nesanta idanuwansa da karatun batsa.

   Domin duk abin da ka karanta indai ba na alkhairi ba ne, yana iya samun naƙasu ga lafiyarka. Allah (s.w.a) Da kansa ya ce "Ka da ku kusanci zina)"

   Da yawa malamai sukan fassara wannan ayar a matsayin duk ƙanƙantar abu, na faɗa ko na gani wadda ya ke bayyana tsaraici yana daga cikin kusantar zina ne.  

   &Allah yasa mu dace, ya nesanta hanyenmu daga faɗawa halaka da kuma nesanta idanuwanmu.


9. Ta ya ki ka tsinci kan ki a kungiyar Marubuta Jigawa wato (JISWA) kuma wane nasarori ki ka samu da kasantuwar ki 'yar cikin ƙungiyar?


9. Shekarar da ta wuce Jiswa ta fitar da gasa a kan cewar iya 'yan jigawa ake buƙata su shiga.

  To a lokacin na samu sanarwar ne ta hanyar @⁨Sadiya Birniwa⁩ daga baya na tambayeta, ta dage da ƙarfafa min gwuiwa a kan na shiga._

  Lokacin ban ma iya rubutun gajeren labari ba, sai a kan wannan gasar na shiga dai.  Daga bisani ta sanar da ni an fitar sakamakon gasa da sunayen labaran da aka shigar.

  Na ce ban gani ba, anan ta buƙaci da na shigo gidan marubutan jigawa.

 To wannan shine mafarin shigata Marubutan jigawa, ban kuma yi ƙasa a gwuiwa ba bayan na shigo na siyi form na zama cikakkiyar 'yar ƙungiya.

  

   Gaskiya na samu nasarori da yawa, mafi muhimmaci shine daga lokacin dana halarci taron Jiswa daga lokacin 'yan gidanmu suka fahimci ba shirme na ke ba.  Na kuma samu ƙwarin gwuiwa a kan na ci gaba da rubutun da nake ba wai aikin banza ba ne.

  Haka nan na koyi wasu dabaru na rubutu da kuma sha'awar yin bigeggen littafi wanda kafin kasancewata 'yar ƙungiyar bani da sha'awar buga littafi sam-sam.

   A kan hakan na ke ƙara miƙa godiyata ga @⁨Sadiya Birniwa⁩ wadda ta dage har sai da na samar da littafin da a yanzu ake kan aikinsa, wanda in sha Allah za a bugashi da kuma yin lounching nasa.


10 Kamar marubuciyar na taba rubutu a fagen fim? In eh me za ka iya cewa game da Bambancin rubutun fim da na zube?


10. Eh gaskiya ina ɗan taɓa rubutun film.

 Gaskiya xan iya cewa rubutun film ya fi sauƙi sosai fiye da na littafi, domin shi komai nasa a sauƙaƙe yake, saɓanin littafi da sai ka bayyana komai, ka fitar da komai da motsinsa.

  Ciki har sai ka bi ƙa'idojin rubutun ma.

  Amma film da ka fitar da magana ta yi daidai ba ruwanka da bibiyar waƙafi ko aya.

  😃😂ƙarin daɗawa kuma ya fi kawo kuɗi 🏃🏻‍♀️


11. Wanne shawarwari za ki bayar wa ƙungiyar Jiswa?


12. Shin ko kina ganin akwai hanyoyi da za a bi a daƙile ko a rage rubutukan batsa?


13. Me za ki iya cewa game da muhimmanci marubuta cikin al'umma? 


14 Tsuntsu mai wayo kin kira shi daya daga cikin labarin da ki ka rubuta a takaitaccen bayani me ya ƙunsa?


15. Shin ko kina da masu tallafa muki a rubutu da za ki iya kiran su da iyayen gida?


Amsa


11. Shawarata ga Jiswa shine ta samar da wani lokaci da zata na shiri a kan rubutu, da kuma koyar da 'ya'yan cikinta yadda rubutun yake. Musamman idan muka yi la'akari da yadda muke da manyan ƙwararru a fanni Adabi da sanin rubutun, haka kuma akwai yaran cikinta da suke da burin son yin rubutun, amma ba su san ta yaya za su fara ba? Ko kuma yadda za su yi rubutun. Misalin dabarun rubutu, banbancin dogo da gajeran rubutu.

  Sannan kuma Jiswa ta ci gaba da ware lokaci domin sauraran matsalolin da 'ya'yan cikinta suke da shi, hakan zai iya taimakawa wajen zama abu ɗaya. Sannan kuma idan da dama Jiswa tana bada wani jinga na aiki a duk lokacin da ta bada darasi ga yaranta, hakan zai zaburar da mutane su farfaɗo daga dogon suman janyewa a rubutun da suke yi. 


12. Akwai hanyoyi kam, idan har za a iya yinsu. A ce akwai wata kafaffiyar ƙungiyar da ke sa ido akan shige da fice na marubuta, idan an samu wadda ke rubutu a kan batsa, a dakatar da rubutunsa, idan ya ƙi hanuwa kuma a yi blocked na layinsa da accnt nasa daga amfani a media.

  Wannan hanya ce mai wahala mai kuma sauƙi idan an jure,_ _kasancewar muna cikin zamani ne na ci gaba, da komai yake xuwa a sauƙaƙe.


13- Marubuci kamar fitila ne da ke haska rayuwar al'umma. Marubuci na iya kawo gyara da kuma hanyoyin warware matsalolin al'umma wadda idan wani ya karanta sai ya ji kamar rayuwarsa aka karanta, kamar kuma an bashi mafita ne a rayuwarsa.

  Wannan kaɗan ne daga cikin gudunmawar da marubuta ke badawa.


14- Kowanne tsuntsu.... Sunan labarin.  

  Labari ne a kan wani saurayi da ƙaddara ta haɗa shi da wata 'yar mai kuɗi har suka yi hatsaniya, a ƙarshe a yunƙirinta na son ɗaukan fansa ta aure shi, ta hanyar shigewa mahaifiyarsa da kuma burin ta kai shi gidansu da ma'aikar mahaifinta dan ta juya rayuwarsa. A ƙarshe auren ya iyu saboda biyyaya sai dai yace ba zai tare a gidansu ba sai dai ta zo gidansu tunda ta ji ta gani, haka kuma ba zata ci cimar gidan iyayenta ba sai irin wadda yake ci.

 

15-Eh tabbas zan iya cewa akwai kam.  

   Sanah Matazu ita ce mutum ta farko da ta fara kawo min gyara a rubutuna, ta kuma koya min abubuwa da yawa a kan harkar rubutu tun ban iya ba da sanin ƙa'idojin rubutu har na zo na iya. Har kuma gobe da nasarar da na samu ina samunta ne bisa dagiyarta da ƙoƙarinta a kan cewar lalai na yi abu, zan iya.

   Sai kuma Yayana Malam @⁨Jiswa Yusuf Abubakar Gumel⁩  da Yayana @⁨Hashim Abdullah⁩ suma sun taimaka min ƙwarai wajen sanin wasu abubuwan da ban sani ba._





1. Da wani lokaci kika fi yin rubutu?

A labaran da kika rubuta ko akwai wanda ya sa ki kuka?


Amsa Safe, yamma, bayan magrib.


2. Wani labari ne da ga cikin labaran da kika rubuta yake sa ki dariya?


2. Eh akwai.


Inuwar Gajimare

Ƙawata ce.

   Waɗannan labaran ina rubuta su ina hawaye.


3. Hanyar Bauchi Film (BIKRA)😃😂Shi kam na sha dariya sosai.



3. Idan kin gamu da ma su karatu wani irin kallo suke miki, wace irin tambaya suka fi miki?


Wayyo Allah! yau ga mu ga Oum-Nass.

  Dan Allah ke ce Oum-Nass? Ke kika rubuta Ismaha zainab? Ke ki rubuta waɗannan litattafan? 

  Ya aka yi kika yi rubutun? Ta ya kike iya tsara rubutun? Shin bakya gajiya, ki wani kike tambaya..?

  &Da dai sauran tambayoyi.


 

Wani irin abinci kika fi so?

😂👌🏻shinkafa da wake



Bayan rubutu ko akwai wani abu ne kike jin cewa da kin sa naci a kansa za ki iya zama ƙwararriya/shahararriya kamar yadda kika shahara a rubutu ko ma fiye da rubutu?


Amsa _Eh akwai.   Sana'ar saƙa Har keken na mallaka na kuma koya.



A duniya yanzu haka akwai marubuta da suke sayar da littafinsu na online su samu manyan kudi kamar marubuciya Carmen Baca, shin a ganinki ta wacce hanya marubutan online na Hausa za su kai ga irin wannan nasarar duba da cewa suna siyar da littafinsu ne ta manhajar WhatsApp a kan kudin da bai taka kara ya karya ba?



Idan suka yi amfani da manhajar zamani kamar Amazon da kuma okada, in sha Allah za su iya yin nasara.

  Ko da ba su kamo shi ba za su samu fiye da nasan.

  Wasu lokutan mu Hausawa mu ke naƙasa kanmu, ko kuma nace mu ke daƙusar da ci gaban mu.



Wanne salon rubutu kika fi jin dadin rubutu da shi, salon da tauraro zai na ba da labarin da kansa ko kuma salon da dan bayan fage ne ke bayarwa?


Amsa _Idan a gajeran labari ne nafi son salon da tauraro ke bada labari.

  Idan kuma a dogo ne nafi fi son salon bayan fags.

  Saboda salon bayan fage na bawa marubuci damar shiga zuciyar jaruman da ke taka rawa a labarin, saɓanin salon da tauraro zai bada labari.


Duk tattaunawar nan da ake Marubuciya ba ta faɗi shekarunta ba. Mu na son ji.


😂😂shekaru ai sirri ne ba a faɗarsu


tambaya ta itace , ku nawa ne wajen maigida km wacce shawara zaki bashi don ya Karo abokiyar zama da zata zame maki mataimakiya a ayyukan gd yadda zaki baje koli kiyi ta rubutunki 🙊


Ni ɗaya ce.

😂😂🤣taɓ! Ai babu ranar shawarar nan. A haka ma ina baje kolin rubutana son raina🚶🏼‍♀️



amatsayinki na marubuciya wacce kika zamo Mai bawa Al,ummah gudummawa daban daban ta rayuwa ta hanyar rubutu shin zaki iya rubutu ko ince zaki iya bada Taki gudummawar ta hanyar yadda mata zasu yarda da cewa kishiya yar uwa ce abokiyar zama ba yadda malam bahaushe ya kirata da kishi ba then wacce hanya zaki bi domin nunawa Al,umma cewa kishi abune Mai matukar sauki ga wacce ta dauka da saukin


Tabbas kam zan iya rubutawa. Musamman idan na yi la'akari da gidan da na taso.

  Tun tasowata mata uku na gani, ba zan iya tuna ga lokacin da suka yi faɗa ba har ake gaba.  Idan har zan iya bada wannan gudunmawar to zan haskawa mutane rayuwar gidanmu ne.






1. Wane quduri ko buri baƙuwar ke da shi a rubutu?


2. Wace alaqa ce ke tsakanin baƙuwar da ƴan uwa Marubuta, kuma ya take kallon sabbin shiga harkar rubutu.


3. Da za ace da baƙuwar, a matsayinki na marubuciya, kawo mana jigo mai muhimmanci da ya kamata marubuta su mayar da alƙalumansu gareshi me za ki ce?


Amsa _1. Na amsa ta.


2. Alhamdulillah, gaskiya ni ina ƙoƙarin kyautata alaƙata da 'yan uwana marubuta, ba laifi kuma tsakanina da su sai sam barka, dan matsala bata taɓa shiga tsakaninmu da su ba.

    Ga sabbin shiga rubutu kuwa ina maraba da su, ina musu kallon ƙannena da suka ɗauko hanyar kawo gyara. Na kan ƙarafafa gwuiwarsu idan hanya ta haɗa ni da su.


4. A yanzu dai kam matsalolin tsaro, illar fyaɗe, shaye-shaye, da kuma taɓarɓarewar zaman aure.


 Waɗannnan jigo guda huɗun sune manyan jigon da a yanzu ya kamata marubuta su yi ƙoƙarin yin rubutu a kansu.





4.  Wacce irin gudummawa kike ganin za ki bayar dan ciyar da marubta gaba?


5. Wacce shawara za ki bawa sabbin marubuta dan rubutunsu ya inganta?


6. Wanne irin cigaba adabi yake samu a yanzu?


7. Wanne irin tufafi kika fi so?


8. Wanne irin buri kike da shi a harkar rubutu?


9. Kafin ki fara rubutu wanne irin kallo kike yi wa marubuta?


10. Shin kin dauki rubutu sana'a ne ko nishadi


4. A duk lokacin da suka buƙaci taimakona ƙofata a buɗe take, mutuƙar na sani.


5- Shine su tsayar da hankalinsu waje ɗaya, kada su gurɓata alƙalaminsu ta hanyar yin rubutun batsa dan neman ɗaukaka.  Idan suka inganta al'amuransu aiyukansu za su yi kyau, za kuma su cimma nasara.

  Kada su yarda da kururuwar farko ta mabiya su ƙi karɓan gyara komai ƙanƙantarsa idan an musu shi. Hakan za sa su kai mataki mai girma na nasara.


6- Yawaitar ɗalibansa da mabiyansa, ina nufin marubuta da mawaƙa.


7- Atamfa.


8- Ban yanke burin ba har yanzu


9-'Yan baiwa.


10-A da nishaɗi a yanzu sana'a.

Comments