Min menu

Pages

Ƙasashe 5 mafiya tsafta da zaman lafiya a Africa

 Ƙasashe 5 mafiya tsafta da zaman lafiya a AfricaAssalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu?


Hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu koda yaushe muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu muna tafe muku ne da jerin wasu ƙasashe guda biyar mafiya zaman lafiya tare da tsafta a Africa.


Idan aka ce zaman lafiya ana nufin gurinda bashi da yawaitar tashe tashen hankula da yawan fadace fadace na daga kabilu ko wasu daga cikin mutane masu tada kayar baya da suke damun wasu daga cikin kasashen dake Africa kamar Nigeria da sauran kasashe.


Sannan kuma idan aka ce tsafta ana nufin gurinda yake tsaf babu wasu abubuwa na kazanta da zasu takurawa mutane na daga dangin abubuwa masu kara ko kuma masu hayaki dadai sauran abubuwa.


Dan haka muje cikin shirin kai tsaye.


Mauritius :- Bincike ya nuna kasar Mauritius kasa ce karama saidai tanada tsafta kuma akwai zaman lafiya da dadin zama.
Ghana :- Kasar Ghana kasa ce babba domin ba karamar kasa bace, kuma kasar ta kasance kasa wacce keda tsafta kuma babu tashin hankali ko yawan fadace fadace a cikinta.
Botswana :- Botswana ma ba wata kasa bace da take da wani girma ko yawan mutane ba domin baza a sanyata cikin manyan kasashen dake Africa ba, amma idan aka zo batun tsafta dole a sanyata domin duk wanda suke zuwa kasar zasu fadi gaskiyar maganata.


Gambia:- Wannan kasar ma tana cikin kasashen da suke da zaman lafiya a nahiyar Africa domin da wuya kuji ana tashin hankali ko wani abu mai kama da fada a kasar.Tanzania :- Tanzania ma kasa ce mai tsafta sannan kuma akwai zaman lafiya kuma akwai gurare masu matukar bada mamaki a wannan kasar domin akwai wani kogi a kasar wand duk wani abu mai rai idan yayi kuskuren taba ruwan kogin take zai daskare ya zama kamar Dutse.Comments