Min menu

Pages

ZIYARAR TA'AZIYYA ZUWA IYAYEN HANIFA ABUBAKAR A KANO!

 ZIYARAR TA'AZIYYA ZUWA IYAYEN HANIFA ABUBAKAR A KANO!Malam Isa Ali Pantami ya samu kai ziyara Kano gidan su Hanifa Abubakar, yarinya 'yar shekara biyar wanda aka kama shugaban makarantarsu kan laifin kisan ta 


Farfesa Pantami ya yi ta'aziyya ga mahaifin yarinya, Malam Abubakar, sannan mahaifin yarinyar ya jagoranci shiga  cikin gida in da ya yi ma mahaifiyar da yan'uwanta ta'aziyya da nasihohi


Malam Ya yi nasiha ga iyayen yarinya mai albarka, akan wajibcin hakuri lokacin jarrabawa mai tsanani irin wannan. Professor Isa Ali Pantami, ya roki Allah Ya sanya Marigayiya Hanifa Abubakar ta zama mai ceto a lahira ga iyayenta, Ya kuma bawa iyayen hakuri akan wannan babban rashi da ya faru sanadiyar wasu azzalumai da suka nuna rashin imani


Iyayen sun yi godiya ga Malam da adduar fatan alheri akan nasihohi da addu'o'i da ya gabata


Comments