Min menu

Pages

 YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETAAkwai hanyoyi masu yawa da mace zata gane idan aljani ya aure ta wasu daga cikin hanyoyin sune wadanda zamu bayyana muku su anan kasa.

1- yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi acikin.

2- a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta

ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al'adarta bane.

3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.

4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba

ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar taba.

5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.

6-‘kin yarda da jima‘i.

7- Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.

8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna.

9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.

10- yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba.

11- yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.

12- jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana dada girma, amma in likitoci suka auna za su ce basu ga komai ba.

13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai.

14- tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha'awar wasu mazan.

15- Jin wari mara dadi yana fito miki ko ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen

gaba.

16- Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba.

17- Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi.

18- In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so suy mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take musu.

19- Za ta dinga yawan zaman a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane.

20- Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.

21- Yawan ciwon kai da yin jiri.

22- Faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa.

25- Iadan mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka

Dadai alamomi da yawa.

Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya doraka akan tsarin maganin da ya dace da kai.

Kuma ka dinga zama da alwala da addu‘o‘in safiya da maraice.

Iadan wannan matsala tay karfi to dole sai an yiwa mutu rukiyyah, an nemi Aljanin an kona shi ko kuma a hada magungunan da za su kashe shi.

Amma dai sihiri da Aljani ba su isa su cutar da kai ba.

Comments