Min menu

Pages

Wata sahara wacce akai shekara 500 ba tare da anyi ruwan sama a gurin ba.


 Wata sahara wacce akai shekara 500 ba tare da anyi ruwan sama a gurin ba.Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai kuma wannan abin da kuke mana yana bamu kwarin gwiwa wajen sake zakulo muku wasu daga cikin abubuwan da muka san zai birgeku.


Kamar yadda kowa ya sani wannan gidan dai gida ne da yake kawo muku labarai da bayanai akan duniya tare da abubuwan dake cikinta walau mutane ko wasu halittun dake rayuwa a cikin duniyar ko gine gine na birane da dai sauran abubuwa.


Yau cikin shirin namu muna tafe ne da sunan wata sahara wacce akai shekara dari biyar ba tare da anyi ruwan sama a cikinta ba.


Sanin kowa ne idan aka ce da guri sahara ana nufin gurin da yake mai tarin rerayi wanda wani ko bishiyoyi babu domin guri ne da ake samun karancin ruwa sannan ake samun tarin rerayi wannan yasa idan lokacin zafi ne gurin yake zama daga cikin gurare masu matukar zafi haka idan lokacin sanyi ne ma zai zama yanada sanyi sosai.

Kuma duk masu wucewa ta gurin za kuga sun tanadi ruwa mai tarin yawa domin gudun samun matsala idan suna tafiya.


Mafiya yawan mutane masu wucewa ta sahara za kuga fatake ne ko kuma mafarauta da suke fita yawon farauta.


Karancin ruwan yana sanyawa tsirrai da bishiyoyi suki fitowa a gun da yake sahara ne saboda koda sun fito mutuwa suke saboda babu ruwa.


Amma duk da haka baza muce babu tsirrai a gurin ba saboda wasu suna daga cikin tsirran suna iya rayuwa a gurin da yake babu ruwa amma dai kalar tsirran da suke iya rayuwar basu da yawa.


Saharar ATACAMA sahara ce mai dadadden tarihi wacce take can a kasar south America bincike ya nuna saharar tana da girman kilo meter 1600.


Ance wannan saharar ita ce saharar da akai shekara a kalla dari biyar ba tare da anyi ruwa a cikinta ba.
Comments