Min menu

Pages

Wata al'ada wacce mace dole ta kwanta da gawar mijinta idan ya mutu.

 Wata al'ada wacce mace dole ta kwanta da gawar mijinta idan ya mutu.Yankin Africa yanki ne wanda ya tara kabilu masu tarin yawa, wanda su kuma wadannan kabilun suke gabatar da al'adu da dama.


Kowacce kabila mata idan mazajensu suka mutu suna gabatar da abubuwa domin nuna jin zafin mutuwar, kasar Nijeriya tana daya daga cikin kasashen da matan al'ummarta ke gabatar da wasu abubuwa idan mazajensu suka mutu, wasu addininsu ne ya koyar yadda mata za suyi idan mazajensu sun mutu yayinda wasu kuma kai tsaye suke abubuwan su


Kamar haka ne ga yan kabilar Igbo inda suma wasu bangare daga cikinsu ke gabatar da abubuwa da dama domin nuna jimami da kuma jin zafi idan mijinsu ya mutu.


Haka nan mace zata kwanta da gawar mijinta domin nuna cewa bata da laifi ko kuma taji zafin mutuwar musamman idan mutuwar mijin nata yazo ne da wasu abubuwa.


Wasu matan ma basa canja kayan jikinsu har tsawon wani lokaci yayinda wasu kan shanye ruwan da aka wanke gawar mijin nasu.


Mu kasance tare daku a wani sabon shirinComments