Min menu

Pages

TA KASHE KANTA BAYAN TA SAMU SABANI DA SAURAYIN TA A JIHAR SOKOTO

 TA KASHE KANTA BAYAN TA SAMU SABANI DA SAURAYIN TA A JIHAR SOKOTOWannan budurwa mai suna Zubaida wadda ake yiwa lakabi da Zube 'yar asulin unguwar Gwuiwa Gawon Kifi a cikin karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto, ta zubawa jikin ta fetur ta kuma kama da wuta inda ta zamo sanadiyar mutuwar ta na barin duniya.


Dan uwan ta ya ce, Zubaida tayi hakan ne sabida sun samu sabani da saurayin ta da ake tinanin zata Aure, wanda ya janyo mata har ta mutu kawo yanzu.


A wani bangare zan tausayawa rayuwar wannan budurwar na yadda Allah (S.W.A) ya jarabce ta da son wani Namiji wanda har zamo sanadin mutuwar ta, sannan kuma wani bangaren Zubaida tayi gangancin kone kanta har ta mutu dalilin ɓacin rai. Mi yasa bata rungumi jarabawa ba❓


Muna rokon Allah yayi wa wannan budurwar gafara, ya kyautata makwancin ta, Allah Ubangiji yayi mata rahama ya yafe mata.

Comments