Min menu

Pages

Nafisa Abullahi Tafice Daga Shirin Labarina, Kalli Sakon Data Aikawa Aminu Saira

Nafisa Abullahi Tafice Daga Shirin Labarina, Kalli Sakon Data Aikawa Aminu Saira

Jaruma Nafisa Abullahi wanda akafi sani da Sumayya cikin shirin Labarina Series ta bayyana ficewarta daga shirin saboda wasu dalilai, a wata takarda data rubuta zuwa ga mai bada umarnin shirin wato Aminu Saira tace baza ta iya ci gaba da fitowa a cikin shirin ba saboda lokaci yayi mata kadan

Tace tana makaranta kuma tana da wani kampani da take kula dashi ga kuma kasuwanci wadannan da wasu dalilai yasa dole za a daina ganinta a cikin Labarina, a karshe tabawa masoyanta hakuri kuma tace itama ba a son ranta hakan yakasance ba.

Sai dai akwai jita jita dake yawo cewa Nafisa Abdullahi sun samu matsala ne da Aminu Saira shiyasa aka daina ganinta a cikin Labarina, amma acikin takardar data aika jaruma Nafisa Abdullahi tace babu wani sabani tsakaninta da Aminu Saira kawai dai bata da lokaci ne


Comments