Min menu

Pages

Manyan dalilan da yasa wasu mazan basa iya gamsar da iyalansu.

 Manyan dalilan da yasa wasu mazan basa iya gamsar da iyalansu.Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokacin ya kuke? Yau cikin shirinmu zamu bayyana muku wasu dalilai da yasa wasu mazan basa iya gamsar da iyalansu.

Mafi yawan lokota maza suna fama da wannan matsala ta saurin inzali,ko saurin kwanciyar gaba,amma sau dayawa idan kaje wajen masi maganin hausa sai ace maka sanyi ne.


Ba tare da tambayoyi akan wasu alamomi da yadda lalurar da samu mutum ba,yayin da ba iya sanyi ne yake jawo matsalar saurin kawowa ba,amma wasu abubuwa da yawa wadan da ma suka fi sanyin tasiri a wannan fanni.
Bangaren cutuka akwai lalurori kama su:1. Hawan jini/Ciwon zuciya.


2. Ciwon Suga.


3. Ciwon hanta 


5. Ciwon koda.
Sannan akwai wasu abubuwan daban kamar su:1. Yawan shan Taba Sigari.


2. Yawan shan giya.


3. Rashin isashshen bacci.


5. Damuwa.


6. Yawan bacin rai.


7. Rashin daidaito tsakanin ma'aurata
Sannan baya ga wannan sau da yawa wasu mazan kafin aure suna iya sanin mace,wani a lokacin daya san mace yasan baya dadewa ko kuma ita macen tace masa bai gamsar da ita ba.
Wanda wannan mutum zai barshi a kwakwalwar sa ya tunanin koda yayi aure ma,bazai iya gamsar da iyalin sa ba wanda hakan zaiyi matukar tasiri wajen haifar masa da rauni da saurin kawowa.
Sannan akwai wadan da idan suna jima'i zaka ga a ransu suke ayyana cewa zasu kawo,shi jima'i aduk lokacin da zaka yi shi ana so ka saka a ranka cewa zaka yishi ne domin jin dadi da kuma gamsarwa, sannan a tika sakawa a ranka zaka gamsar da iyalin ka. Sannan ka rika cire fargabar cewa ba zaka iya gamsar da ita ba,sannan ka rika kwantar da hankali kuka a rika wasanni sosai kafin a ce ka shige ta,domin hakan ne zai saka sha'awar ka ta motsa sosai gaban ka ya tsaya yadda ya dace.
Sannan a dena dogara da magani hayin kusantar iyali,domin dogara da magani shine zai saka ya zama baka da karfin gwiwa a duk lokacin da zaka kusanci iyali,domin zaka saka a ranka cewa maganin nan shine yake baka karfi da kuzari,amma a yanzu tunda baka sha ba zaka iya kawowa da wuri.wannan tunanin da kake gayawa kwakwalwar ka shine zai saka naza ka gamsu ba. A takaice wadan nan sune abubuwa da suke hana da Namiji gamsar da mace a lokacin saduwa. Insha Allah a bayani da zamu kawo na gaba zamu kawo abubuwan da suke hana jin dadin jima'i tsakanin mace da Namiji.


Comments