Min menu

Pages

Wasu Tagwaye da aka Haifa Amanne sun Samu Aiki Bayan Iyayensu sun Gujesu

sohna and mohna

Wasu Tagwaye da aka Haifa Amanne sun Samu Aiki Bayan Iyayensu sun Gujesu

Wasu tagwaye masu suna Sonha da Monha wanda aka haifa A Manne sun samu aikinyi a wani daga gwabnatin Kasar India bayan iyayensu sun gujesu, An dauke su aiki tare tunda baza a iya rabasu ba sannan za ana biyan su albashi duk wata,

Sonha da Monha wanda suka gama karatun Diploma a matakin wanda suka karanta abin daya shafi fannin wutar lantarki sun samu aiki daza ana biyansu dubu Ashirin a kudin kasar India (Rs 20,000), tagwayen sun girma ne a wani yankin kasar indiya mai suna Pingalwar

Suwa Nene Sonha da Monha?

Sonha da Monha wasu tagwaye ne 'yan kasar India da aka haifa a hade wato jikinsu guda ne amma kayuwa guda biyu garesu wanda hakan yasa ake kawatantasu a matsayin mutum biyu, kamar yadda rahoto ya bayyana tagwayen suna da zuciya gida biyu, hannaye hudu, huhu da koda duk guda biyu, amma kafafunwasu biyu ne kacal

Suna da duk abin dazai tabbatar da cewa mutum biyu ne su amma kafafuwa na mutum daya ne garesu, tun farkon haifuwar su a shekarar 2003 liktoci sunyi kokarin rabasu sai dai angano cewa idan aka raba su daya zai rasa ransa,

Iyayen Sonha da Monha sun gujesu tun suna jarirai, wanda hakan yasa aka dauki nauyinsu karkashin kulawar wata kugiya mai kula da mutane masu matsala irin tasu, sunyi rayuwa cikin kulawa tarfe da daukar nayin karatun su wanda yanzu kuma aka basu aikinyi

Sonha da Monha sunyi godiya bayan samun aiki daga gwabnati wanda suka kira hakan a matsayin wata dama da aka basu domin suma za suyi rayuwa kamar sauran mutane, kuma sun samu aiki ne a fannin da sukayi karatu wato abin daya shafi wutar lantarki

Comments