Min menu

Pages

Kabilar da suke datse yatsun hannunsu idan dan uwansu ya mutu domin tayashi jin zafin mutuwar.

 Kabilar da suke datse yatsun hannunsu idan dan uwansu ya mutu domin tayashi jin zafin mutuwar.Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai, kuma wannan yana dada bamu kwarin gwiwa wajen sake zakulo muku labari da muka san zasu birgeku.


Yauma cikin shirin namu munzo muku ne da labarin wata kabila wacce mutanen cikinta ke yanke wani sashe na yatsun hannunsu domin nuna jin zafi idan dan uwansu ko yar uwarsu sun mutu.


Kafin muje cikin shirin idan kai sabon shigowa ne wannan gidan kana yawan ziyartarmu domin samun sabbin shirye shirye.


Kamar yadda kuka sani al'ada ita ke haska mutane har a gane yadda suke, kuma kun sani kowacce kabila al'adunta sunsha banbam dana wata kabilar.


Kabilar Dani wata kabila ce dake papua a can New Guinea wanda kidayar shekara ta dubu biyu da tara ta nuna mutanen cikinta sun haura dubu ashirin da biyar kunga kenan zuwa yanzu sun karu da kaso mafi tsoka.


Kabilar Dani kabila ce da mutanen cikinta suka kware wajen noma da kiyo sannan suna gabatar da abubuwan su kamar na arnan daji domin basa rufe jikinsu da kaya saidai idan maza ne su sanya wani kyalle ko kuma wata fata ko ganye su rufe tsiraicinsu yayinda mata suma ke rufe gabansu ne kawai da kuma wani sashe na kirjinsu.


Kabilar suna gabatar da wani abu na cire wani sashi na yatsun hannunsu domin taya Dan uwansu jin zafi ga  idan ya mutu domin su sunce duk mutumin daya mutu to azaba ake masa.


Hakan yasa suke yanke wani sashi na yatsun hannunsu domin taya mamaci jin zafi, idan mace nada miji ko Dan da ta haifa ya mutu to zata yanke wani sashi na yatsanta sannan idan wani ma ya sake mutuwa zata sake yankewa, hakama ga maza.


Mu kasance tare daku a wani sabon shirin idan wannan bayanin yayi muku kuyi share.


Comments