Min menu

Pages

Hukumar Custom ta sanar da ranar da zata fara horas da sabbin jami'anta.

 


Nigerian Custom Service (NSC) ta sanar da ranar da zata fara horar da sabbin jami'anta wadanda aka gama tantancesu.


Ta sanar da cewa zata fara bada horon ne a ranar Litinin 10 ga watan Janairu shekarar 2022 a makarantar horarwa da ke Kano da kuma Lagos.


Bayar da horon an kasashi ne kashi-kashi inda masu matsayi na 03, 04 da 06 za su samu horo a makarantar horaswa da ke Goron Dutse a Kano, inda masu matsayi na 08 za su samu horo a Ikeja da ke Lagos.


Ana so ko wanne ya tabbatar ya zo ranar Lahadi 9 ga watan Janairu 2022.


Allah Ya bada Sa'a.

Comments