Min menu

Pages

Kabilar da basa wanka sannan sunfi kowacce kabilar kyau...

 Kabilar da basa wanka sannan sunfi kowacce kabilar kyau...



Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci barkanmu da sake saduwa tare daku a wannan website din, muna godiya sosai.


Idan muna tafe tare daku a wannan gidan muna kawo labarai da tarihi a bangaren tarihin duniya. Yau muna tafe muku da wani tarihi na wata kabila wadda tunda suke basu taba wanka ba amma ana nuna sunfi kusan dukkan kabilun Afrika kyau.


Kabilar Himba wata kabila ce mai karfi da suke zaune a wani yanki a kasar Nambia sannan suna matukar kishin al'adarsu dan haka suka riketa da hannu bibbiyu.


Bayan haka kabilar himba  suna barin duk wani bako daya ziyarce su yayi tarayya da mata idan na miji ne sannan in mace ce itama zata tara da na miji ba wani abin damuwa a ciki.


Kabilar Himba noma suka rike a matsayin sana'ar su sannan mata sayar da abinci da ruwa.


Basa wanka da ruwa saboda yadda yanayin yankin nasu yake, to saidai koda yake basa wankan amma jikinsu baya nuna irin sunyi datti sosai.


An rawaito cewar kasar Nambia kasa ce data tara mutane masu matukar kyau a duk Afrika sannan sunada ruwa wanda ake samun kifaye masu yawa a ciki kuma sunada manyan dajika masu yawa.


Kabilar Himba na daga cikin kabilar da suka rike noma da kiyo da mahimmanci musamman kiyon awakai raguna da sauransu.



Comments