Min menu

Pages

IZZAR SO EPISODE 67 ORIGINAL BAKORI TV

 IZZAR SO EPISODE 67 ORIGINAL BAKORI TV


Shirin izzar so wanda tashar bakori tv take kawo muku shiri ne mai dogon zango wanda ya tara jarumai maza da mata.


Shirin an nuna yadda ake gabatar da wata harkar kasuwanci ne a kamfanin shinkafa na wani hamshakin mai kudi mai suna Alh matawalle.


Hamshakin mai kudin ya dauki wata yarsa ce kwaya daya Mai suna Hajiya Nafisa Matawalle ya dorata akan ita ce shugabar kowanne ma'aikacin dake cikin wannan kamfanin nasa.


Yarinyar ta taso da salo na jiji da kai tare da raina mutane duk girmansu, bata ganin mutumcin kowa.

Ana haka ne aka kawo mata wani sabon accountant mai suna Umar Hashim. Wanda shi kuma tun daga ranar da aka kawo shi ya nuna bazai iya daukar duk wani raini ko cin kashin da take yiwa sauran ma'aikata ba.

An bayyana Umar Hashim a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, wannan yasa duk wasu ma'aikata dake wannan gurin suke matukar kaunarsa.


Dan haka ya samu daukaka agun kowa, wanda wannan daukakar daya samu ba karamin batawa hajiya Nafisa rai tayi ba wannan dalilin yasa take ganin kota wanne hali sai tayi yadda zata wulakantashi.

Yanzu dai shirin izzar so episode 67 ake ciki bayan an gabatar da izzar so episode 66 satin daya gabata.Karfe goma za'a saki shirin izzar so episode 67 yau dan haka ku kasance tare damu

Comments