Min menu

Pages

Idan aka haifi tagwaye kashe su akeyi a wannan kabilar

 Idan aka haifi tagwaye kashe su akeyi a wannan kabilar



Wato yin karatun halayyar wasu kabilu abu ne da zaisa mutum ya zauna shi kadai yana nazari saboda saboda labarin wasu kabilun suna da matukar abin mamaki wanda idan mutum yaji zai jima yana mamakin faruwar hakan.

Labarin wata kabila nazo da ita yanzu wacce su idan har aka haifa musu yan tagwaye wato yan biyu basa yadda kashe su suke ta hanyar binne su da ransu.


Saboda su a tunaninsu kamar haihuwar yaya biyu a tare kamar wani aiki ne marar kyau ko kuma shafin shaidanu ne.


Kabilar koma a Nigeria take kuma tana daya daga cikin kabilun da basu da yawa a duniya suna zaune ne cikin duwatsu a wani yanki dake jihar Adamawa wani guri da yake iyaka tsakanin Nigeria da kamaru.


A takaice dai wannan gurin da kabilar koma take yana tsakanin kasashen nan ne guda biyu Nijeriya da kamaru.


Wani abin mamaki ga kabilar basa sanya kaya a jikinsu kamar yadda muke yi, mata suna sanya ganyen bishiya ne ga jikinsu yayinda mazan suke samun dan wani abu su rufe kafadunsu dasu.

Har ila yau kabilar basa amfani da ashana wajen kunna wuta saidai suyi amfani da dutse wajen gogashi da wani dutsen har wuta ta kama.


Sannan idan mata ta mutu a wannan kabilar to kanwarta ce zata gaji duk abinda ta mutu ta bari, sannan shaye shaye tsakanin matan wannan kabilar ya zama ruwan dare.

Babban abin mamaki da al'ajabi a wannan kabilar shine yadda suke kama yayan tagwaye da aka haifa a hada da mahaifiyarsu a binne da ransu wai domin a wanke dattin kasa wanda su ganinsu wannan haihuwar tasu da akai ya jawowa kasar kazanta wanda idan basuyi saurin binne wadannan tagwayen ba kamar wani abu maras kyau zai iya samunsu.
 

Comments