Min menu

Pages

Yadda zaku cire kudi akan ATM Machine koda baku je da katin ATM din ba.

 Yadda zaku cire kudi akan ATM Machine koda baku je da katin ATM din ba.Wani lokacin ana samun damuwa sai kuga mutum yayi tafiya har zuwa kan ATM Machine domin ya cire kudinsa sai yasa hannu a aljihunsa ko kuma tasa hannu cikin jakarta in mace ce sai kawai taji ATM card din bayanan ta manta shi gida ko kuma ya manta shi a gida, wanda wannan zaisa dole saidai mutum ya hakura da cirar kudin ya koma gida ya dauko card din ATM din nasa sannan ya dawo ya kuma cire kudin.


Idan akai rashin dace ya rasa ATM card din kuma shikenan saidai ya hakura ya jira harya same shi, saboda koda gurin masu POS yaje domin yi musu transfer idan ba sun san mutum ba basa karbar transfer yanzu saboda masu yin damfara ta hanyar tura fake alert.


To yau cikin hukuncin ubangiji munyi iya bakin kokarin mun gano wasu hanyoyi wanda zaku iya cire kudi akan ATM Machine koda kunje ba tare da ATM card dinku ba.


Idan kana amfani da access bank ga hanyar da zaka bi ka cire kudinka koda ka manta ATM card dinka


Ga masu amfani da access bank sai su danna wannan number  *903# a Sim din da sukayi register a Bank din nasu wato wanda suke jin alert sai ku zabi gurin withdrawal money, daga nan saika sanya adadin kudin da kake bukatar cirewa sannan kasa pin dinka wanda kake amfani dashi.

Zasu tura maka sako ta message sun tura maka code Dan haka saika zabi access bank ATM machine, ina nufin kaje gunda machine na access bank yake saika danna 0 akan machine din domin kayi withdrawal din kudinka ba tare da ATM card ba.

Daga nan saika zabi access money, saika sanya number wayarka ko taki, tare da kudin da kake bukata sannan kasa wannan code din da suka tura maka ka danna continue, ka jira kadan za kaga an fito maka da kudinka.


Sai kuma masu amfani da fidelity bank suma ga yadda za suyi

Kawai ka danna *770*8*amount# da layin da kayi register fa bawai da wani ba,domin idan bada Sim din bane bazaiyi ba.


Zasu baka dama ka zabi one time pin wato OTP sai ka sannan pin din bank din  domin kayi wannan transaction din.

Dan haka code din da suka tura maka dashi za kayi amfani, Dan haka sai kaje kan ATM Machine ka danna kowacce number ne saika zabi paycode cash out ko kuma ka danna 4cash.

Sannan saika danna wannan pin din na OTP da suka tura maka saika sanya adadin kudin kamar yadda muka koyar a baya, shikenan zasu turo maka da kudinka.

Sai kuma masu union bank suma ga hanyar da za subi su cire kudinsu ko babu ATM card akan ATM Machine

 
Kawai ka danna *826# sai kai generating na paycode tare da pin sai kabi hanyar da muka nuna a baya saika sanya pin din akan machine din sannan ka zabi paycode sannan kabi hanyar ta karshe wanda zasu rubuta maka shikenan saika cire kudinka.


Sai kuma wanda yake amfani da UBA shima ga yadda zaiyi


Da farko za kayi amfani da layin da yayi register dashi a Bank din naka wato wanda ka bude account din dashi sannan saika danna *919*30*amount# zasu tura maka gurin da zaka zabi pin din sannan da inda zaka sanya paycode dinka zasu tura maka code na cash out ta layin wayarka kai tsaye saika je kan ATM Machine din ka zabi paycode cash out,  saika sanya cash out code dinka saika sanya adadin kudin da kake bukata sannan ka danna Ok bayan sun tabbatar da transaction dinka yayi verified to zasu tura maka kudinka.


Wannan kenan sai kuma sauran ba bank din da zamu kawo muku nan gaba idan mun gama bincike a kansu.


Comments