Min menu

Pages

Shin gaskiya ne zancen da ake yadawa cewar WhatsApp zai rufe account din mutane idan basu tura wani sako ba?

 Shin gaskiya ne zancen da ake yadawa cewar WhatsApp zai rufe account din mutane idan basu tura wani sako ba?Karanta kuji .........


Daga Jiya Zuwa yau jama'armu Hausawa Suna ta yada wani recording ta hanyar Forwarding a group group na whatsap dauke da muryan wani mutumi.


Mutumin yana cewa acikin Recording din wai kamfanin Whatsap zai rufe Account na mutane ma damar basu yada zancen nashi ba, Da sauran zantu ka dai marasa tushe........


to a gaskiyar magana wannan sakon ba gaskiya bane wani kato ne kawai yatsaya ya kirkiri labarin, irin mutanen nan ne masu hada hoto da voice suce idan baka tura group kaza ba zaka hadu da wani abu. ko suce idan katura zaka samu wani abu..


Kamfanin whatsap yana da shafi a twitter, yana da Shafi a facebook, Amma dika basu bada wannan sanarwa ba kawai sai wani wanda sunan mai kamfanin whatsap din ma baya iya fada ne zai bada sanarwan!!!


Idan kamfanin whatsap zai tura masu hulda dashi sako. yana iya tura musu kaitsaye ta shafukansu na whatsap kuma tare da alamar da yake nuna daga kamfanin whatsap dinne. ko su turawa kowane mai hulda dasu sako ta hanyar status yadda kowa yana hawa zaiga sakon daga sama wajen status dinsa.


Gaskiya jama'a yakamata muna gane abubuwa na shirme, da yaudara, da damfara a social media fa. Mudaina Forwading na kowane abu da muka gani batare da tabbatar da Sahihancin sa ba.


Zancen whatsap zasu rufe account na mutane karya ce tsagwaronta wasu suka hada. masu yadawa kuma suyiwa Allah su daina.

Comments