Min menu

Pages

An bani kyautar naira million dari biyar domin na daina yiwa Buhari waka amma naki karba.

 An bani kyautar naira million dari biyar domin na daina yiwa Buhari waka amma naki karba.Shahararren mawakin siyasar nan da yayi suna wato Alhaji Dauda kahutu Rarara yace an bashi kimanin kudi har million dari biyar domin ya daina yiwa Buhari waka amma bai karba ba.


Ya kara da cewa akwai mutanen da suke masa kallon ko idan an bashi kudi zai iya rabuwa ko daina yiwa Buhari waka dan haka suke nufo gurinsa da wasu kudade domin su sanya ya daina yin wakar.


Ina so mutane su sani bawai dan kudi nake yiwa Buhari waka ba ina masa ne saboda yadda naga ya dace kuma mutum ne mai kaunar talakawa da tausayinsu sannan kuma suma talakawan suna kaunar sa dan haka nake masa wadannan wakokin domin kowa ya tabbatar da cewa Buhari mai gaskiya ne.


Kuma ina kira mutane su daina yimin tallan kudi da niyyar na daina yiwa Buhari waka domin bazan karba ba.


Nafi son Buhari fiye da kudi 

Comments