Min menu

Pages

Halayen ka irin na Annabawa ne, ka cigaba da abubuwan Alkhairi da Kasa a gaba>>Jawabin Sarkin Daura ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

 Halayen ka irin na Annabawa ne, ka cigaba da abubuwan Alkhairi da Kasa a gaba>>Jawabin Sarkin Daura ga Shugaban Kasa Muhammadu BuhariMai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk ya taya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari murnar kammala Babbar Sallah, inda yace halayen Shugaba Buhari irin na Annabawa ne.


Alhaji Faruk Umar Faruk ya bayyana Haka, jim Kadan bayan kammala Sallah a Masallacin Idi na Kofar Arewa dake Daura.


Ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu akan dumbin aikace-aikacen dayake shimfidawa a garin Daura, Katsina dama Kasa baki daya.


Mai Martaba Sarkin Daura yace Masarautar ta dauki nauyin rubuta wani Littafi akan dukkanin aikace-aikacen da yayi lungu da Sako na Nigeria, inda yace za'a mika shi ga Gwamnatin da zo domin dorawa daga inda ta tsaya.


Ya kara dacewa, Mutanen Daura zasu cigaba da addu'o'i ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin dorewar cigaba da dumbin ayyukan Alkhairi dayake shimfida wa a Kasar.


Alhaji Faruk Umar Faruk ya bayyana cewa, kasancewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi Mulkin Soji dana farar hula, wannan ne ya sanya yake ta shimfida ayyukan Alkhairi a Kasa.


Jim Kadan bayan kammala jawabin, Shugaba Muhammadu Buhari ya yanka rago ga kanshi da Kuma Yan Nigeria

Comments