Min menu

Pages

AN NEMI BUHARI DAYA WAIWAICI YAN KASUWA AKAN TSADAR KAYAN ABINCI DOMIN A SAUKAR DA FARASHIN SU


AN NEMI BUHARI DAYA WAIWAICI YAN KASUWA AKAN TSADAR KAYAN ABINCI DOMIN A SAUKAR DA FARASHIN SUMaigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya don girman Allah ka waiwaici 'yan kasuwa, musamman masu sayar da shinkafa da masara da dawa da gero


Bincike ya nuna, barayin da suke satar dukiyar Gwamnati, suna tsoron ajiye kudi a banki saboda binciken EFCC, idan an girbe amfanin gona sai su saye abinci su boye, sai anzo lokaci irin wannan suke fitarwa su sayar da tsada


Don Allah Maigirma shugaban kasa ka waiwaici 'yan kasuwa, ka ayyana dokar ta baci akan price control, ana barin 'yan kasuwa suna kuntatawa al'umma, kullun sai kara farashin kaya abinci suke yadda suka ga dama, muna sayan abu yau, kafin wayewar gari sun kara farashi sai kace tamkar babu Gwamnati


Ya kama shugaba Buhari ka yiwa azzaluman 'yan kasuwa marassa imani magana da yaren da zasu gane, ko kuma ka basu fomula irin wacce kayi amfani da ita lokacin mulkin soja kasa sojoji suna fasa shagunan miyagun 'yan kasuwa a wancan lokaci


Due process akan matsala na price control ba zai yiwu ba a halin da muke ciki, kafin abi due process tsadar rayuwa ta halaka adadi mai yawa na talakawa da zasu mutu da yunwa, Wallahi Billahi ni shaida ne akwai wadanda suke kwana da yunwa, akwai wadanda a rana sau daya suke samu suci abinci


Mutum zai iya yin hakuri akan komai amma banda yunwa, ya kamata a dauki matakin gaggawa don girman Allah


Yaa Allah Ka kawo mana sassauci, Ka amintar damu daga zaluncin 'yan kasuwa

Comments