Min menu

Pages

Duk wanda aka kama da kakin sojoji bashi da bambanci da yan ta'adda

 Duk wanda aka kama da kakin sojoji bashi da bambanci da yan ta'addaDuk wani da yake sanya kakin sojoji bashi da bambanci da yan ta'adda dan haka baza mu lamunci wannan shirmen ba..


Zamu zuba ido sannan zamu dau mataki mafi muni ga duk wanda muka kama yana sanye da kayan sojoji kuma muka tabbatar da cewa ba sojan bane..


Shugaban sojoji janar faruk shine ya fadi wannan maganar..

Idan baku manta ba a yan kwanakin nan aka nada janar faruk a matsayin sabon shugaban sojojin kasa na Nijeriya kuma tunda aka nada shi ya fara aiki tukuru domin ganin an kawar da duk wasu yan ta'adda da suka addabi wannan kasar wannan yasa ya fara sanya dokar hukuncin kisa ga duk wani da aka kama yana rike da bindiga..

Bayan ya sanar da wannan dokar kuma ya sake cewa duk wani da aka kama sanye da kayan sojoji a hukunta shi..

Hakika wannan dokar da sabon shugaban sojojin yazo da ita zata taka rawa sosai a bangaren masu tada kayar baya..

Comments