Min menu

Pages

Da Ɗumi Ɗuminsa: CBN Zai Karya Farashin Shinkafa A Kasuwanni

 Da Ɗumi Ɗuminsa: CBN Zai Karya Farashin Shinkafa A Kasuwanni

    


A wani sabon yunƙuri don magance hauhawar farashin kayan abinci a kasuwanni, Babban Bankin Najeriya (CBN ) da ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) sun kammala shirye-shiryen raba tan dubu 27,000 na shinkafa mai bawo (Paddy) ga kamfanonin sarrafa shinkafa ƙasa baki ɗaya.

 

Rabon shinkafan da za a yi a rumbunan ajiyan RIFAN da ke faɗin Jihohi 16 daga yau Alhamis ya biyo bayan sayar da shinkafar da manoma suka yi a baya a matsayin biyan bashin kuɗin noman ‘Anchor Borrowers ‘(ABP) da suka karba ga masu sarrafa shinkafa a yayin Dalar shinkafa da aka yi a jihohin Neja, Kebbi, Gombe da Ekiti.


A cewar mukaddashin Daraktan sashin hulɗa da jama’a na Babban Bankin, Osita Nwanisobi, an zabi jihar Kaduna a matsayin babban wurin da za a ƙaddamar da rabon shinkafar wanda za a yi a lokaci daya kuma a jihohin da aka fi samu ingancin noman shinkafa a kakan da ta gabata.


Ya ce, wannan sabuwar dabarar ta yi daidai da hurumin Bankin na tabbatar da daidaiton farashi da kuma mayar da hankalinsa na kasancewa babban bankin al’umma.


Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwar cewa rabon shansheran zai haifar da faɗuwar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya, tare da bunƙasa samar da kayayyaki, sannan a ƙarshe a duba ayyukan dillalan da ke neman haifar da karancin kayan abincin ta hanyar samar da abincin.


A kwanan nan Babban Bankin na CBN ya gabatar da Dalar shinkafa a jihohin Neja, Kebbi, Gombe da Ekiti, tare da Babban Birnin Tarayya, Abuja da Ebonyi da Kuros Ribas waɗanda suma za a gabatar da nasu Dalar a makwanni masu zuwa a cikin abin da Bankin ya ce yana daga cikin gudummawar da yake bayarwa don tabbatar da samar da wadatar abinci a Najeriya

Comments