Min menu

Pages

Ya kamata Mal Gumi ya fada mana gaskiya dawa yake tare, yan Nijeriya ko yan Bindiga

 Ya kamata Mal Gumi ya fada mana gaskiya dawa yake tare, yan Nijeriya ko yan BindigaMutanen Nigeria sun fara maganganu akan shehin malamin nan da yake shiga cikin jeji domin yin sulhu da yan bindiga.


Tun lokacin da malamin ya fara shiga jeji wasu da dama daga cikin yan kasar ta Nigeria suka fara tofa albarkacin bakinsu wasu su nuna hakan da yake yayi daidai domin ta dalilin shiga jejin da yake yasa yan bindiga da dama sun ajiye makamansu tare da tuba sannan sun saki mutanen da sukai garkuwa dasu.To saidai irin wannan mu'amular da malamin yake yi tare da yan bindigar yasa wasu ke zarginsa duk kuwa da cewa har yanzu babu wata hujja da ta nuna malamin yana tare da yan bindigar.


Maganar da malamin yayi a jiya akan a bewa yan bindigar da sukayi garkuwa da wasu shine abinda ya tada kura har aka fara magana mai zafi akan malamin wasu na ganin bai dace malamin yayi wannan maganar ba kwata kwata.


Har wasu ma ke cewa anya kuwa malamin yana tare da yan Nijeriya?


Dan haka suke da bukatar su san ko tsakanin yan kasar da yan bindigar malamin wa yafi so

Comments