Min menu

Pages

Asirin kasar America ya fara tonuwa game da kashe musulman da ake a Palasdine

 Wata yar majalisa ta fito ta fadawa duniya yadda kasar america ke sayarwa Isra'ila makamai suna kashe musulmiKasar Amurka ta sayarwa Isra'ila da makamai na dalar Amurka $735m domin ta yaki Palasdinawa~Inji Alexandria Ocasio-Cortez


Allah ya fara tonawa kasar Amurka asiri a yakin da kasar Isra'ila take yi da kasar Palasdinawa.


Wata 'yar majalisa a Amurka mai suna Alexandria Ocasio-Cortez ta fito fili ta bayyana cewa, duk jinin da aka zubar a Palasdin, to tabbas kasar Amurka tana alhaki akan wannan.


'Yar majalisar ta bayyana cewa, makaman kare dangi na dalar Amurka $735m gwamnatin Amurka karshin jagorancin Joe Biden ta sayarwa Isra'ila ba tare da amincewar mu ba.


Alexandria ta ci gaba da cewa" sanadin wannan yau an wayi gari mun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da raba wasu da gidajen su". Inji ta.


Ya Allah ka isar ma al'ummar musulmi ga kasar Amurka da Isra'ila.Comments