Min menu

Pages

An sanar da wasu gurare a arewa masu matukar hatsari a Nijeriya

 Wasu gurare masu matukar hatsari a Nijeriya Akwai takaici matuka a bayyana arewa a matsayin wani yanki da yafi matukar hatsari wannan kuma ya faru ne saboda wasu al'amura da suke faruwa a kasar musamman arewa.


Yan uwa barkanmu da wannan lokacin sannan sannunmu da sake haduwa tare daku cikin wannan gidan mai albarka na duniyar labarai.


Muna matukar jin dadi yadda kuke kasancewa tare damu koda wanne lokaci dan haka mun gode sosai da sosai.


Kamar yadda muke kawo muku wasu bayanai da al'amura da suka shafi kasa Nijeriya dama sauran kasashe, yau muna tafe ne da bayani akan wani yanki da bincike ya nuna yanada matukar hadari.Guraren an bayyana sune kan gaba wajen hatsari yanzu domin da zarar mutum ya tafi wannan guraren to za kuga hankalinsa dama na sauran mutanen da suka sanshi a tashe yake saboda ana tunanin komai kan iya faruwa dashi.


Dan haka zan sanar daku wadannan guraren kamar yadda binciken ya nuna.


Borno jihar borno kusan itace ta farko a wuraren da aka bayyana sunfi hatsari saboda rashin tsaron daya addabi jihar, kuma an bayyana jihar kusan itace matattari ta yan boko haram dan haka da wuya ayi wasu kwanakin ba tare da anji labarin anyi wani abu ba a yankin.


Yobe kusan idan ka dauke maiduguri jihar yobe itace ta biyu wajen hadari a tafiye tafiye dan haka aka bayyanata cikin guraren da suke da hatsari.


Zamfara tun zuwan wasu masu tada kayar baya wanda suka fitini yankuna da kashe kashe babu dalili zamfara ta zamto jihar da take da hatsari saboda wadannan mutanen sun samu gindin zama a jihar sannan sun takurawa mutanen dake jihar da dauke dauken mutane sannan su nemi kudin fansa idan an biya shikenan idan kuma ba'a biya ba su kashe mutum dan haka itama wannan jihar an sata cikin guraren masu hatsari.


Adamawa wannan jihar ma tayi kaurin suna wajen tashe tashen hankula na yake yake da yan boko haram dan haka itama ta zamto jiha mai hatsarin gaske.


Kaduna yanzu itama wannan jihar ta zamto abar tsoro saboda bayyanar wasu yan bindiga da suke daukar mutane sannan su kashe in ba'a biya kudin fansa ba wannan yasa itama jihar aka sanyata cikin guraren masu hatsarin gaske.


Niger jihar nan itama yanzu sai a hankali saboda abubuwan da ake fuskanta na rashin tsaro da tashe tashen hankula dan haka itama ta zamto jihar da aka ce tana daga cikin guraren masu hatsari.

Comments