Min menu

Pages

Yan tawayen da suka kashe shugaban kasar chadi sun nemi sulhu ga sabon shugaban kasar

 Yan tawayen da suka kashe shugaban kasar chadi sun nemi sulhu ga sabon shugaban kasar.Sunce a shirye suke su mika wuya domin ayi sulhu a wannan lokacin inji shugaban yan tawayen Mahdi Ali.


Wannan na zuwa ne lokacinda sabon shugaban kasar chadi wato mahamat Idris dabby ya lashi takobin daukar fansar ran mahaifinsa da aka kashe kafin karshen lokacin da aka bashi na mulkar kasar domin cewa yai idan harda sauran numfashi a kirjinsa dole sai ya dauki fansar kashe mahaifinsa da yan tawayen sukai.


To ana haka ne kuma saiga kira ga yan tawayen cewar suna neman sulhu daya hakura su zauna dashi domin su sasanta.


In baku manta ba yan tawayen sune sukai sanadin mutuwar shugaban kasar chadi a kwana biyu da suka wuce wanda har aka nada dansa mahamat Idris dabby.


To har yanzu dai ana zaman jiran jin ta bakin dan gidan shugaban kasar.

Comments