Min menu

Pages

Labari mai dadi ga yan Nijeriya

Labari mai dadi ga yan Nijeriya hukumar NDE ta fara biyan ma’aikatan SPW Ƙaramin Ministan ƙwadago Festus Keyamo ya bayyana cewa ma’aikatar kuɗi ta tarayya ta saki wasu kuɗi domin fara biyan matasa dubu 774,000 da gwamnatin tarayya ta ɗauka aiki na watanni uku ƙarƙashin shirin SPW da hukumar NDE.


Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwar manema labarai da ya wallafa a shafinsa na Twitter Hausa Daily Times ta samu ranar Asabar.


Ministan ya ce ya bada umarnin fara gudanar da bincike kan asusunan waɗanda za a biya su kuɗin don gudun biyan waɗanda basa cikin tsarin domin sun gano wasu matsalaloli a tattare da wasu asusuna.


“Ma’aikatar kuɗi ta saki wasu kuɗi don fara biyan ma’aikatan SPW, kuma na umarci da a tsaurara bincike a kan asusun waɗanda za a biya kafin a fara biyan kuɗin.


“Mun gano wasu mabanbanta asusun banki na haɗe da lambar BVN ɗaya, wasu asusun kuma bayanan dake cikin BVN ɗinsu bai yi daidai da bayanan dake asusun bankin su ba, yayin da wasu BVN ɗin su ma babu shi dadai sauran su”. Inji Keyamo.


Ya kuma bayyana cewa bisa ƙudurin su na ganin cewa sun daƙile yin zamba, ya uamrci hukumar NDE wadda shirin ke ƙarƙashinta da ta rubuta wa bankunan da su magance waɗannan matsaloli kafin a biya ma’aikatan da asusunsu ke bankunan su.


Ya bayyana cewa, a yanzu haka bankin ACCESS ne ya cika ƙa’idojin da hukumar NDE ta gindaya domin har an fara biya.


“A halin yanzu Bankin Access ne kawai ya cika sharrudan biyan waɗannan kuɗi domin har ya gabatar da asusan ma’aikatan bayan an tabbatar babu wata matsala kuma NDE ta fara biyan waɗannan asusu na bankin”. A cewar Festus Keyamo.


Ya ƙara da cewa, suna jira su ji daga sauran bankunan Zenith, UBA, FCMB, Fidelity, Heritage da Bankin Yobe Micro-Finance suma su tsabtace waɗannan matsaloli da muka gano domin su ma su fara biyan ma’aikatan.


A watan jiya ne dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin fitar da kuɗi domin biyan matasan da dubu 774,000 da aka ɗauka aikin SPW wata uku d

Comments