Min menu

Pages

Boko Haram ta tilastawa Mutane Sama da 90,000 Hijira zuwa Nijer


 Kungiyar Boko Haram ta tilasta wa mutane Sama  90,00 tsallakawa kasar Nijar daga Jihar  Borno

Sama da mutane 90,000 ne suka yi gudun hijira daga garin Damasak na jihar Borno zuwa Jamhuriyar Nijar a ranar Laraba, bayan yawan hare-hare da ƴan Boko Haram ke kai musu.


Wata majiya daga gwamnati ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa akalla mutane 10 suka rasa rayukansu, da yawa sun samu raunuka, dubunnai sun fantsama cikin daji don kubutar da rayukansu bayan harin na ranar Laraba


Rahotanni sun shaida cewa maharan sun kone daruruwan gidaje, shaguna, gine-ginen gwamnati ciki harda caji ofis, a harin na ranar Laraba wanda Kuma shi ne karo na 6 a cikin mako 2 da ƴan Boko Haram suka kai a garin na Damasak.


Har lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa ta musamman daga rundunar soji, sai dai rahotanni daga majiyar Duniyar labarai sun bayyana cewa tuni ƴanta’addan sun kafa tutarsu a garin tun ranar Larabar kuma suna cikin garin har zuwa yanzu


Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments