Min menu

Pages

Wata Sabuwa An Karrama Kamfanin Yin Giya a Kaduna

An kara  Karrama Kamfanin yin Giya A Matsayin Wanda Ya Fi Kowanne Biyan Haraji A Kaduna


hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta karrama Kamfanin Giya na Nigerian Breweries da kyauta mafi girma a matsayin wanda ya fi biyan haraji a jihar.


Shugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar ne ya bayyana kamfanin a matsayin wanda ya zama zakaran gwajin dafi yayin wata walimar karramawa da aka gudanar a Kaduna ranar Juma’a


Shugaban ya yi kira ga sauran hukumomi da kamfanoni su kwaikwayi kamfanin wajen biyan harajinsu yadda ya kamata ba tare da an tursasa musu ba.


“Makasudin bayar da wannan kyautar shine domin mu zaburar da mutane su ci gaba da biyan harajinsu domin samun ci gaba da bunkasa rayuwar al’umma.”


Da yake gabatar da kyautar ga Manajan kamfanin na Nigerian Breweries a jihar, Mista Abbay Ajayi, Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi ta jihar, Murtala Dabo ya yabawa kamfanin saboda ficen da ya yi.


Da yake karbar kyautar, Mista Ajayi ya ce kamfanin nasu ya biya kudaden harajin da suka kai kusan Naira biliyan 330 a cikin shekaru biyar da suka gabata ga Najeriya, wanda daga ciki jihar ta Kaduna ta amfana da kusan Naira biliyan daya da miliyan 400 tsakanin 2018 da 2020.



 

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments