Min menu

Pages

Wata budurwa ta taso takanas daga lagos zuwa Abuja gun saurayin da suka hadu a facebook saidai labarin baizo da dadi ba

 Ta taso tun daga legas domin taga masoyinta da suka jima suna soyayya saidai kash labarin baiyi dadi ba.Wata yarinya budurwa yar kimanin shekaru ashirin da biyar yar asalin lagos ta taso takanas domin ta kawowa saurayinta da suka jima suna soyayya ziyara.


Budurwar tace sun hadu da saurayin nata ne a dandalin sada zumunta na facebook wanda suka jima suna murza soyayya.


Tace bazata manta ranar da suka hadu da saurayin nata ba a facebook.


A ranar masoya ta a ranar muka hadu dashi kuma muke soyayya kamar ma hadiye juna tsakanina dashi a cewar budurwar.


Tsananin soyayyar da muke dashi ne yasa nace zan kawo masa ziyara shi kuma yace zai bani duk kudin da na kashe da zarar na karaso garin da yake.


Muna yin waya tun ina hanya shi kuma yace yana nan yana jiran nazo, to amma tun da na karaso shikenan na kira wayar tasa naji a rufe kuma bansan inda yake ba domin bai fadamin unguwa da layinsu ba a cewar matar.


Daga karshe dai mutane ne suka hada mata kudi akan ta koma inda ta fito.


Bayan sun nuna mata rashin dacewar ziyarar tata duk da cewa itan ba musulma bace.


Masu karatu me zaku ce?

Comments