Min menu

Pages

Sanarwar daya kamata duk yan Nijeriya su sani daga gwamnatin tarayya

 Gwamnatin tarayya ta fitar da wata sanarwa mai mahimmanci ga yan Nijeriya Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa ga yan Nijeriya game da allurar rigakafin korona da aka kawo kasar.


An sanar da cewa bai zama dole ga yan kasar cewa lalle dole sai sun amince anyi musu ba, ganin damar yan kasar ne in sunada ra'ayi zasu iya cikewa ayi musu.


Gwamnatin tace ba takurawa ga duk wani wanda bai amince da allurar ba dan haka in kuna da ra'ayi kuje ai muku allurar rigakafin.


Saidai gwamnatin tace yin allurar rigakafin yanada matukar amfani sosai dan haka yanada kyau kuje ai muku amma fa ba dole inji gwamnatin tarayyar.


Mun samu wannan sanarwar daga ministan lafiya olorinnumbe mamora da ake tattaunawa dashi a gidan talabijin na Arise tv.


Babu wani abu daya zama dole zabi ne kawai idan mutum yanada ra'ayi yaje ai masa in kuma bashi shikenan inji olorinnumbe din.


In baku manta ba a yan kwanakin nan ne aka kawo allurar rigakafin korona Nijeriya daga kasar waje domin a yiwa yan kasar.

Comments