Min menu

Pages

Abin birgewa daya kamata duk dan Nijeriya ya sani akan tutar Nijeriya da kuma wanda ya fara zanata

Ku kalli wasu abubuwa na birgewa ga wanda ya fara zana tutar NijeriyaYan Najeriya sanannu ne daga kasashen da ake matukar la'akari dasu a matsayin masu kwalkwaluwa da ilimi a kaf fadin duniya. 


Yan Najeriya sunyi fice Daga kan abubuwan ilimi, fasaha harma abubuwan gwaninta na birgewa harma sun zama ababen koyi da girmamawa a wasu bangarorin ilimi.


Anan zamu kawo muku abubuwan burgewa dangane da mutumin daya zana Tutar Najeriya.


Taiwo Akinkumi shine Wanda ya zana Tutar Najeriya. 

Akinkumi ya zana Tutar Najeriya a lokacin da yake da shekara 23 sannan a matsayin dalibi a London. Akinkumi ya zana Tutar a shekarar 1959, Akinkumi ya taba cewa asalin Tutar Najeriya Wanda ya zana a sashen dake dauke da fari wanda ke a tsakanin korayen zanen guda biyu akwai hoton rana.

A yanzu haka yana da shekaru 84, sannan injiniya ne Wanda yayi ritaya daga aikin gwamnati.

Comments