Min menu

Pages

WATA SABUWA ABDULJABBAR YAYIWA MALAMAN KANO DA ZASUYI MUKABULA BAKIN ALBISHIR

 WATA SABUWA ABDULJABBAR YAYIWA MALAMAN KANO DA ZASUYI MUKABULA BAKIN ALBISHIR
Sheikh Abduljabbar ya cika baki yin mukabala da duk malaman dake kalubantarsa.A wata shira mai tsawon minti hudu da akayi da Malamin nan na Kadiriyya Abduljabbar a sashen Hausa na BBC.


Malamin ya cika baki kan cewa duk wani malami dayake tunanin abin dayake fada ba gaskiya bane ya tareshi suyi mukabala.


Malamin dai a kwanan nan gwamnatin kano ta dakatar dashi daga yin wa'azi tare da rufe makarantarsa dayake koyar da karatu akan zarginsa da wa'azi Wanda keda alaka da tada fitina, malamin mutane da dama sunsha zarginsa yanayin karatuttuka wanda bayayiwa yawancin musulmai dadi.

 Bayan rufe makarantarsa da hana shi wa'azi da akayi yace ba'a masa adalci ba idan ba'a bashi dama ya kare kansa ba, ya zargi gwamnati da kokarin tauye masa hakki, haka kuma Malamin yace dakatar dashi daga yin wa'azi ba komai bane face bashi dama da akayi ya sami lokaci yayi ta rubutu irin Wanda bazaiwa malamai masu ja da maganganunsa dadi ba.

 Inda a cikin maganarsa yake cewa: inawa maluman nan bakin albishir dasu saurareni zanyi ta fitar rubututtukan da bazai musu dadi ba har sai sun rasa inda zasu saka Kansu. 


A yanzu dai haka gwamnatin kano ta fitar da lokacin da zata hada mukabala tsakanin Abduljabbar da malamai dabam dabam daga ko wane bangare domin tabbatar wa da malamin kuskurensa ta fuskar ilimi.


Kungiyar izala wanda ta dade tana gogawa da malamin sunyi matukar farin ciki da wannan hukunci da gwamnatin kano ta zartar saboda sun dade dama suna zargin malamin dayin batanci ga sahabbai masu daraja a cikin wa'azin dayake gudanarwa. A yanzu dai haka an baiwa malamai dama dasu je su shirya domin wannan mukabala.

Comments