Min menu

Pages

Karon batta! Iyayen daliban da aka sace sun shiga daji neman yayansu da kansu

 Karon batta! Iyayen daliban da aka sace sun shiga daji neman yayansu da kansuIyayen yaran da aka sace a makarantar GGSS Jangebe sun yanke shawarar shiga daji domin nemo 'ya'yansu da aka sace da Kansu.

A yau ranar juma'a 26 ga watan February ne aka sami wasu yan bindiga sunyi awun gaba da yara yan makaranta a Jangebe dake a jihar zamfara, wannan na zuwane bayan mako daya da sace dalibai maza da akayi a jihar Neja. Karo na uku kenan yan bindiga na awun gaba da dalibai a Najeriya.

BBC HAUSA tace wasu daga cikin iyayen yaran sun sheda mata cewa sufa bazasu jira gwamnati ba,sun shiga daji domin ceto 'ya'yansu da Kansu daga hannun yan bindigan.

Yanzu gaba dayan garin Jangebe ne muka tasanma barayin yaran ko amu ko a  su inji wani matashi da aka sace da kannuwansa biyu a cikin yaran da aka sace.

A yau juma'a ne dai aka tashi da sabon tashin hankali a jangebe dake jihar zamfara dangane da sace dalibai da wasu yan bindiga sukayi.

Wannan dai na zaman  daya daga cikin manyan garkuwa da mutane da akayi arewa maso yammacin Najeriya, wannan al'amari dai ya zama tamkar wani wasan kwaikwayo ta yadda ake sace daliban kuma bayan an dawo dasu a kwashi wasu.

Dangane da wannan ko wane mataki gwamnatin Najeriya zata dauka?

Comments