Min menu

Pages

Ina nemawa yan bindinga gafara daga gun gwamnatin tarayya inji Mal Abubakar Mahmud Gumi

 Ina nemawa yan bindinga gafara daga gun gwamnatin tarayya inji Mal Abubakar Mahmud GumiShehin malamin nan ya nemawa yan bindingar gafara daga gwamnatin tarayya, sannan yace hakika yanada kyau gwamnati ta amince tayiwa duk dan bindingar daya ajiye makaminsa afuwa tunda dai zaman lafiya ake nema a kasa.


Yace yan bindingar sunata korafi akan cewa ana kashe wadanda basu ji ba kuma basu gani ba sannan ana lahanta wasu wanda ba sune masu laifi ba.


Kusan wannan shine yafi takura mana har muke yawan daukar makamin inji yan bindingar.

Malamin ya fadi hakane bayan sunyi zama da yan bindingar lokacinda ya shiga cikin jejin sakamakon dauke wasu dalibai da akayi a kwanan nan.

Tun lokaci mai tsawo ake yawan samun tangarda tsakanin yan bindingar da mutanen gari ta inda sai suyi ta shiga gari suna kashe mutane tare da dauke wasu, hakan shine yasa malamin ya kuduri niyyar shiga duk jejin da yan bindingar suke yana zama dasu tare da yi musu wa'azi, inda da dama daga cikinsu suke ajiye makamansu suna tuba tare da cewa baza su kara aikata wannan mummunan laifin ba.

Hakan yasa suka nemi Malam daya nema musu afuwa daga gwamnatin tarayya tunda dai sun ajiye makamansu.

Hakika wannan malamin yana kokari sosai da yake shiga jeji domin yin nasiha ko wa'azi ga yan bindingar.

Comments