Min menu

Pages

gwara ƴan ta'adda suci gaba da ta'addanci akan su shiga izala


 Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi 


Gaskiya Mal. Ɗahiru Bauchi Maganganun ka sunyi Muni Matuƙa, 

Ana hira dashi game Ta'addancin da masu garkuwa da mutane sukeyi, Da cikin abubuwan da ya kawo ya kawo cewa" Ƴan uwa fulani kashedin ku da shiga ƙungiyar Izala ƙungiyar maƙiya annabi.


Har yana ishara da cewa" Da ka shiga izala gwara ka tsaya ka cigaba da ta'addancin ka, Domin Laifin kisan kai da ƙwace dukiyar mutane, bata kai laifin Ƙin annabi ba.

Ƴan izala ba musulmi bane, Ba ku guje su da dai sauran munanan kalamai.


Allah Ya shiryar damu.


Wallahi wannan ita ce aƙidar da suke karantar da almajiran su tsawon lokaci hatta a littafan su, Musamman game Babban Malamin muaulunci Ibnu Taimiyyah Da Sheikh Ibnu Abdulwahab Allah ya masu rahama.


Lallai Ashe aikin Dr Ahmad Gumi Ya tsolewa Hatta Ƴan Gargajiya ido da ƴan bidi'ah da azzaluman Shuwagabanni da malamai ido, Aikin da ya kamata suyi, Shine aka samu wani ya fara yi, Sai Hasaada ta biyo baya.


Lallai ba sai an gayawa duniya suwaye mabiya annabi ba, Ahlussunnah su suka fi Kowa kusa da Annabi, Da yi masa biyayya da damuwa da addini da yaɗashi, 


Mu ba soyayya kawai muke ba, A'a aiki muke kamar yadda Allah ya bamu umurni 


إن أولى الناس بإبراهيم للذين اتبعوه وهذا النبي والذين آمنوا والله ولي المؤمنين  


Duk rikicin mu da ƴan bidi'ah a tsakanin soyayya da biyayya ne, Mu muna son Annabi muna masa biyayya, Su kuma suna sonsa basa masa biyayya.


Amma lallai Waɗannan kalmomi da Shehi yayi sun munana matuƙa kuma ya kamata ya tuba.


Muna Roƙon Allah daya shiryar da wannan tsoho da mabiyansa damu baki ɗaya.

Allah ka shiryi waɗannan ƴan ta'adda, Ka tsare harasan mu da diga digan mu daga zamiya.

Allah ya shirye ka ka gane kuskure da guɓa da kake fesawa al'umma Amin.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments